CORONAVIRUS: Matakan yadda Najeriya za ta sake bude kofar tattalin arzikin ta -Sakataren Gwamnati

0

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya bayyana cewa za a bi daki-daki wajen sake bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Tattalin arzikin Najeriya ya tsaya cak tsawon makonni hudu, bayan hana zirga-zirgar jiragen sama, rufe makarantu, masana’antu da cibiyoyi.

An kuma kulle jihohin Lagos da Ogun da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Boss Mustapha ya yi wannan karin haske ne a wurin taron manema labarai a kan ci gaba da Kwamitin Yaki da Coronavirus ya ke samu a kullum.

Ya ce za a dauki tsawon makonni shida ana bude wurare, wato za a dauki matakai sai uku kenan tsawon duk bayan kowane mako biyu.

Ya ce za a dauki matakan ne domin a rika bi sannu a hankali ana sassauta wa jama’a kuncin rayuwar da suka fuskanta dalilin wannan dokokin hana zirga-zirga da tsayawar da tattalin arziki ya yi cak.

“Za a dauki matakan ne domin saukake wa jama’a halin kuncin da suka shiga.” Inji Saataren Gwamnatin Tarayya, wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa mai yaki da cutar Coronavirus.

Ranar Litinin da ta gabata ne Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana sassauta dokar Abuja daga 9 na safe zuwa 6 na yamma. Amma kuma za a daina zirga-zirga daga 8 na dare zuwa 6 na safe daga ranar 4 Ga Mayu, 2020.

“Amma kuma duk da wannan sassauta doka, za a rika bi ana yi wa jama’a gwajin cutar Coronavirus tare da zakulo wadanda ake zargin sun kamu da cutar.” Haka Shugaba Buhari ya kara jaddadawa.

Shi kuma Boss Mustapha, ya yi kira ga jami’an tsaro da su tabbatar da cewa su na tirsasawa ana kiyayewa da sabbin matakan da za a dauka.

Wannan doka dai ta takaita zirga-zirga da dare daga 8 na dare zuwa 6 na safe, ta shafi dukkan jihohin kasar nan.

Sama da mutum 1,700 ne suka kamu da cutar a Najeriya. Abuja ne birmi na biyu wajen yawan masu cutar, sao Lagos ta farko da kuma Kano ta uku.

Share.

game da Author