CORONAVIRUS: Juventus za ta killace Ronaldo kwanaki 14

0

Rahotanni daga birnin Turin, inda kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta ke a kasar Italy, sun tabbatar sa cewa kungiyar za ta killace fitaccen dan wasan ta, Cristiano Ronaldo da zaran ta diro kasar daga hutun da ya ke yi a kauyen su na haihuwa, Madeira a kasar Portugal.

Jaridar Tuttosport, The Sun ta London, Goal.com da manyan jaridun duniya sun wallafa cewa Juventus ta yi shiri tsaf domin killace duk wani dan wasan kulob din da ya tafi kasar sa hutun Coronavirus idan ya dawo kasar.

Cikin ‘yan wasan da ake sa ran killacewa kafin Ronaldo, sun hada da Douglas Costa, Danilo da wasu da ake jin za su dawo kafin Ronaldo.

Ronaldo ya shafe tsawon wata guda cur ya na hutu a garin haihuwar sa Madeira, inda ya karfi hayar wani gida da ke bakin ruwa, shi da ‘ya’yan sa da farkar sa Georgiana su na kwana ciki a kullum a kan kudi fam na Ingila €3,500.

Mahukuntan Juventus sun duk wani dan wasan da ya tafi hutu, idan ya dawo na za a bari ya gwamutsu da sauran ‘yan wasan ba sai ya yi kwanaki 14 a killace.

Wani labari mai kama da wannan kuma ya tabbatar da cewa Hukumar Shirya Gasar La Liga ta Spain har ta tanadi wani kamfanin gwaji mai suna SNYLAB domin ya yi wa ilahirin ‘yan kwallon La Liga na kungiyoyin Spain da ma’aikatan su gwajin Coronavirus kafin a koma ci gaba da gasar nan da watan Yuni.

Ita sai Juventus ce ke kan gaba a gasar Seria A, amma da sauran wasanni 12 da ba a karasa ba tukunna.

Cutar Coronavirus ta hargitsa gaba dayan harkokin kwallon kafa a duniya. Ta karya kungiyoyi da dama, kuma tuni da yawa sun rage wa ‘yan wasa, kociya da sauran ma’aikatan kulob-kulob din albashi.

Cikin wadanda suka dandana azabar Coronavirus har da kociyan Manchester City, Pep Gordiola, wanda ya rasa mahaidiyar sa.

Haka shi me tsohon shugaban kungiyar Real Madrid, cutar Coronavirus ta kai shi barzahu.

Cikin makon da ya gabata ne PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Jose Mourinho da David Moyes suka koma yin tukin-wucin-gadi, su na raba abinci ga marasa galihu saboda zaman gidan da aka tilasta jama’a na yi don kauce wa Coronavirus.

Share.

game da Author