CORONAVIRUS: Jihar Nassarawa ta fatattaki matafiya da suka shigo jihar daga Kano

0

Shugaban Karamar Hukumar Keffi, Abdulrahman Sani-Maigoro, ya shaida wa manema labarai cewa jami’ai sun kama wata mota kirar Sharon dauke da matafiya daga Kano, kuma duk ta umarce su su juya su koma inda suka fito.

Sani-Maigoro ya ce baya ga wadannan matafiya jami’ai a karamar hukumar sa sun kama wasu motoci da suka shigo Keffi daga Kano da Legas, amma fa ba barsu sun ko taka burki ba suka fatattake su su koma inda suka fito.

Ya kara da cewa mutane su daina yada jita-jita kamar wadda ke yawa a yanar gizo cewa yan kasuwa daga Kano da Legas suna shigowa garin da dare sumin cin kasuwa.

A karshe ya ce karamar hukumar za ta ci gaba da sa ido domin kare mutane daga yadawar cutar coronavirus.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata gwamnatin jihar Nasarawa ta bayyana cewa daga yanzu duk wani matafiya da ya dawo jihar daga jihohin Kano da Legas sai an killace shi na tsawon kwanaki 14.

Gwamna Abdullahi Sule na jihar ya shaida haka a taro da yayi da sarakuna da shugabannin addinai na jihar.

Ya ce hakan ya zama dole ganin yadda ake cin gaba da samun karuwar yaduwar annobar Coronavirus, sannan kuma hakkin gwamnati ne ta kare mutanen ta.

Ya umarci sarakunan su tabbata an killace duk wani matafiyi da ya ratso ta jihar daga Legas ko Kano.

Gwamna Sule ya ce ko da ko ‘yan uwan mu ne, muddun dai daga Legas ko Kano suka dawo a tabbata an dakatar dasu an kuma killace su na kwanaki 14.

Share.

game da Author