CORONAVIRUS: Jihar Katsina ta tara Naira miliyan 241

0

Kwamitin yaki da cutar COVID-19 na jihar Katsina ya bayyana cewa ta tara Naira miliyan 241 daga gudunmawar da mutane da kungiyoyi suka ba da domin yaki da coronavirus a jihar.

Shugaban kwamitin Mannir Yakubu ya sanar da haka ranar Juma’a a taron manema labarai da aka yi a garin Katsina.

Ya ce a asusun kwamitin na da tsabar kudade da ya kai Naira miliyan 205.7 sannan sauran Naira kimiyan 33.5 alkawurra ne.

Ya ce kwamitin za ta yi amfani da wadannan kudade, wajen bude asibitocin kula da masu fama da cutar guda 3 a jihar.

Yakubu ya ce za a yi amfani da kudaden wajen horas da biyan ma’aikatan kiwon lafiyan da za su kula da masu fama da cutar.

Sannan a wayar da kan mutane game da cutar.

Bayan haka Yakubu ya ce gwamnati ta sa a kebe wurare a manya-manyan asibitocin dake Daura, Baure, Malumfashi, Dutsinma, Kankia da Jibia a matsayin wuraren kula da masu fama da cutar.

Ya ce a yanzu dai mutane 9 ne ke dauke da cutar, daya ya mutu a jihar.

An gano mutum 8 a karamar hukumar Daura daya a Dutsenma.

Yakubu ya ce gwamnati ta sa a rufe duk kasuwanin dake jihar domin hana yaduwar cutar.

Ya yi kira ga mutane da su Kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar domin kare kansu da makusantan su daga kamuwa da cutar.

Yanzu mutum 442 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 152 sun warke, 13 sun mutu.

Share.

game da Author