Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya amince da rokon da Gwamnatin Najeriya ta yi, na neman bashin dala bilyan 3.4, domin gaggauta ayyukan farfado da tattalin arziki kasa.
Manyan Daraktocin Bankin IMF ne suka amince da rokon wannan bashi d Najeriya ta nemi a ba ta da gaggawa, domin yayyafa wa tattalin arzikin kasar ruwa daga sumar da cutar Coronavirus ta sa ya yi.
Wannan ne makudan kudade mafi yawa da Bankin IMF ya bai wa wata kasar Afrika lamuni tun bayan barkewar Coronavirus.
Baya-bayan nan IMF ya bai wa kasar Ghana lamunin dala bilyan 1.
Ranar 6 Ga Afrilu ne Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta ce Najeriya ta kaddamar da gidauniyar neman yadda za ta harjadp naira bilyan 500 domin amfani da kudin a buga wa tayoyin motar tattalin arzikin Najeriya, wadanda suka sacce tun bayan barkewar cutar Coronavirus.
Kokarin hakan ne ya sa Najeriya ta garzaya garzayawa har Bankin IMF domin neman rufin asiri.
Daga nan Zainab ta ce sauran hanyoyin samun kudaden sun hada da bashin dala bilyan 2.5 daga Bankin Duniya sai kuma wani bashin na dala bilyan 1 daga Bankin Bunkasa Kasashen Afrika (AfDB).
Zainab ta ce za a yi amfani da bashin IMF da na Bankin Duniya domin a yi cike gibin matsalar kudi da ta rufta wa Najeriya, tun bayan da asusun kudin wajen kasa ya kusa yin karkaf.
Sannan kuma da kudaden ne idan an karbo za a talmalmala a gudanar da wasu ayyukan kasafin kudi, ganin cewa hakan ne kadai mafiya, tunda farashin danyen mai ya fadi warwas, kamar farashin karan taba sigari a duniya.