CORONAVIRUS: Gwamnatin Tarayya ta aika da tirelolin abinci 110 Kano

0

Ministar Harkokin Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq, ta bayyana cewa gwamnati ta aika da tireloli buhunan abinci 110 zuwa jihar Kano. Minista Sadiya ta ce za araba abinci a wasu kebabbun wurare guda biyar da gwamnati ta ware.

Idan ba a manta ba gwamnatin Tarayya ta umarci da a maida hankali Kano domin dakile matsalolin da ta fada a kwanakin baya.

Shugaba Buhari ya sanar da garkame jihar na tsawon Kwanaki 14 domin a gano bakin zare game da aikin gwajin cutar coronavirus da kuma yin bincike kan mace-macen da aka rika samu a kwanakin baya.

Minista Sadiya ta ce abincin da za a raba sun hada da masara, dawa da gero. Ta ce an aika da tirelolin shinkafa har 100 a makon da ya gabata domin rabawa talakawa a jihar.

A karshe ta hori shugaban hukumar agaji ta Kasa, Mustapha Maihaja ya tabbata mutane sun samu abinci kamar yadda gwamnati ta bayar wato a raba yadda ya kamata.

Share.

game da Author