Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanar da dage takunkumin zamna gida dole na awa 24 kullum zuwa Kwanaki biyar banda ranakun Talata da Laraba daga wannan Mako.
Amma kuma a wannan sati, za a huta zaman gida ne daga ranar Laraba da Alhamis. daga nan kuma sai a koma Kulle sai talatan makon gobe.
Sanar da gwamnati ta saka a shafukan ta ta Tiwita ta ce daga wannan mako mutane za su rika walwala a ranakun Talata da Laraba zuwa 12 n dare.
A jawabin da mataimakiyar gwamnan jihar Hadiza Balarabe ta yi ranar Laraba, 1 ga watan Afrilu ta ce mutane za su garzaya kasuwa su
jida abinci zuwa gida.
Bayan nan gwamnati ta yi kira da a tabbata ana bin doka kamar yadda aka saka a jihar.
Idan ba a manta ba, an tabbatar da mutum 3 a jihar Kaduna da suka kamu da cutar coronavirus da ya hada da gwamnan jihar, malam Nasir El-Rufai.
Jihar Legas ce take kan gaba da wadanda suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya. Sai kuma bbabn birnin tarayya Abuja, sai kuma jihohin Osun, Bauchi da wasu jihohi.
Discussion about this post