CORONAVIRUS: Gwamnatin Buhari ta raba wa mutane 130,000 naira bilyan 2.6 a Jihar Katsina

0

Gwamnatin Tarayya ta raba kudaden tallafi ga marasa galihu na jimlar naira bilyan 2.6 a Jihar Katsina.

Da ya ke bayani a lokacin wani taron manema labarai, Mashawarcin Gwamna Aminu Masari a fannin Inganta Rayuwar Al’umma, Rabe Nasir, ya ce an raba kudin ne bisa tsari da umarnin Shugaba Muhamadu Buhari, inda ya ce a tallafi marasa galihu a wannan yanayi na zaman killace jama’a saboda annobar Coronavirus.

Ya ce an raba wadannan ikahirin kudade ta tsarin tura wa marasa galihu kudade a asusun bankin su, wato ‘Conditional Cash Transfer’.

Rabe ya ce kudaden dama ariyas ne tun daga watan Janairu, Fabrairu, Maris da Afrilu, wadanda Buhari ya ce duk a hada jimilla a biya lokaci daya.

A kan haka, ya ce an tantance magidanta 133, 225, kuma an raba kudaden ga 130, 000 tukunna.

Daga nan sai ya ce a Jihar Katsina akwai Gwamnatin Tarayya na kashe naira milyan 473 a duk wata ta na ciyar da ‘yan makaranta 338, 488 daga makarantu 1,407.

Ya ce an dauki hayar masu dafa abinci har su 4097 masu dafa abincin da ake ciyar da daliban na firamare.

Da juya barun N-Power kuwa, Nasir ya ce ‘yan jihar Katsina 13, 478 ne amfana a matsayin aikin wucin-gadi.

A karshe ya ce mutane 8,364 suka amfana da lamunin Tradermoni a Jihar Katsina.

Share.

game da Author