Gwamnatin jihar Bauchi ta saka dokar hana zirga-zirga na tsawon kwanaki 14 a jihar.
Gwamnatin ta yi haka ne domin dakile yaduwar cutar coronavirus a jihar.
Idan ba a manta ba a ranar Talata ne jihar ta sanar da karin mutum daya da ya kamu da cutar coronavirus.
Mutumin da ya kamu da cutar na da shekaru 57 sannan har an aika dashi asibitin koyarwa na Jami’ar Tafawa Balewa domin a ci gaba da kulawa da shi.
Gwamnan jihar Bala Mohammed na daga cikin mutane uku din da suka kamu da cutar a jihar.
Gwamna Bala Mohammed da ke kwance a asibiti ya Sanar da dokar hana walwala a jihar yana mai cewa dokar zai fara aiki ne ranar Alhamis biyu ga watan Afrilu 2020 da karfe 6 na yamma.
A dalilin haka duk iyaloki jihar za a rife su.
Sannan domin rage wa mutane wahalan talauci yayin da suke zaman gida za a sassauta dokar ranar Asabar da Laraba na kowace mako daga karfe 10 na safe zuwa 4 na yamma saboda su rika fita domin siyan kayan abinci da kayan da za su bukata.
Duk masu harkoki da ya shafi al’umma ba za su zauna a gida ba.
Gwamnati ta yi kira ga mutane da su ga wannan mataki da gwamnati ta dauka a matsayin hanyar dakile yaduwar coronavirus a jihar.
Idan ba a manta ba a ranar Litini ne Shugaban Kasa Mohammadu Buhari ya saka dokar hana shiga da fita garin Abuja, Jihar Legas da jihar Ogun.
Shugaba Buhari ya ce, hakan ya zama dole a dakatar da shiga a wadannan jihohi da babban Birnin tarayya domin dakile yaduwar cutar coronavirus a jihohin da Abuja.
A wannan lokaci babu wanda za a bari ya shiga wadannan garuruwa ta sama ko kasa.
Discussion about this post