CORONAVIRUS: Gwamnan Bauchi ya fasa yanke albashin ma’aikata, bayan ya sha caccaka kamar kuibin jaki

0

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed, ya janye shirin yanke albashin ma’aikatan jihar da ya yi niyyar yi, domin ya tara kudaden yaki da cutar Coronavirus a jihar.

Janyewar ko fasawar ta faru ne bayan an rika suka, ragargaza da caccakar sa a fadin jihar kamar kuibin jaki.

PREMIUM TIMES a ranar Talata ta buga labarin yadda aka rika ragargazar gwamnan tare da nuna rashin amincewar ma’aikatan jihar a cire musu albashi.

Mataimakin Gwamnan Jihar, Bala Tela ne wanda kuma shi ne Shugaban Kwamitin Yaki da Coronavirus na Jiha, ne ya bayyana aniyar cire wa ma’aikatan jihar wani yanki na albashin su har tsawon watanni uku a jere.

Ya sanar cewa gwamnati ta amince a rika cirar wani kaso na albashin ma’aikatan jihar, tun daga kan Kwamishinoni har Kananan Ma’aikatan Gwamnati.

Ma’aikatan jihar da dama da suka zanta da PREMIUM TIMES, sun ce sun ki amincewa a cire musu albashi ne, saboda ba a tuntube su ba kuma ba a shawarce su ba.

Sai dai kuma ganin yadda ya ke shan ragargaza, Gwamna Bala ya ce ya umarci Akanta Janar na Bauchi ya dakatar da shirin yankar kudaden daga albashin ilahirin ma’aitakan jihar.

Daga daga kakakin yada labarai na gwamnan, Lawal Ma’azu ne ya sanar da wannan dakatar da cirar kudaden.

Share.

game da Author