Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed bai daddara da kamuwa da cutar Coronavirus ba, wadda sanadiyyar ta ya killace kan sa fiye da sati biyu, bayan ya kamu da cutar.
Fitar Bala ta farko ya zarce Babban Masallacin Juma’a na Bauchi da ke Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi, inda ya gwamutsu da dimbin jama’a bayan an gama sallar Juma’a.
Gwamnan, wanda a lokacin da ya killace an nuno bidiyon sa ya na jawabi ga al’umar Jihar, har ya ja kunnen su cewa su rika kaffa-kaffa da shiga cikin rincimin jama’a, saboda Coronavirus gaskiya ce, ba abin wasa ba ce.
Sai dai kuma ya bai wa mutane da dama mamaki inda kasa da awa 24 bayan an sake fitar da sakamakon gwajin sa karo na biyu, kuma an tabbatar da ya warke, sai ga shi a cikin dandazon jama’a a masallacin Juma’a.
Tun kafin a yi Sallah dama a rigaya an tanadar masa wurin zama a sahun gaba, tare da Sarkin Bauchi.
Bala bai dauki darasi ba, kuma bai yi amfani da kiran da ya yi wa jama’a su rika kaffa-kaffa ba, duk kuwa da cewa wasu mutane biyar ne suka kamu da cutar bayan cakudu da Bala.
Bayan an tashi daga Masallaci, Bala ya gaisa da Sarkin Bauchi da malaman addini, kuma ya yi wa jama’a godiya.
Ya isa masallacin sanye da takunkumi da kuma safar hannu.
Idan ba a manta ba, a lokacin da Bala ke a kilace, Mataimakin sa Baba Tela ya nuna takaicin yadda al’ummar Jihar Bauchi ba ta damu da yin kaffa-kaffa da cutar Coronavirus ba, duk kuwa da dubun dubatar mutanen da ta kashe a duniya.
Discussion about this post