A ranar Litini ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya Sanar cewa gwamnati ta kara wa ma’aikatan gwamnatin jihar hutun kwanaki 14.
Ganduje ya ce gwamnati ta yanke wannan shawara ne bayan ta saurari rahotannin kwamitin tara kudade domin tallafawa talakawa da gajiyayyu a jihar.
Ya ce yin haka zai taimaka wa gwamnati wajen shirya marakan hana yaduwar cutar coronavirus a jihar.
“Muna kira ga mutane da su kiyaye dokar hana walwala da gwamnati ta saka sannan a yawaita wanke hannaye, tsaftace muhalli da rage yawan shiga taron mutane.
Ganduje ya ce har yanzu iyakokin jihar za su ci gaba da zama a rufe sannan gwamnati za ta tallafa wa talakawa da gidajen marayu da kayan abinci.
Ganduje ya kuma yaba wa asibitin kula da wadanda za su kamu da cutar coronavirus da gidauniyar Dangote ke ginawa a jihar.
Ana gab da kammala gina asibitin wanda zai dauki akalla mutum 500.
Idan ba a manta ba a ranar Litini ne Hukumar Hana Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta sanar cewa mutane shida sun kamu da cutar coronavirus a kasar nan.
NCDC ta ce sakamakon gwajin da ta yi ya nuna cewa an samu karin mutum 8 daga jihohi 3 da Abuja a kasar nan.
2 a jihar Kwara, 2 Edo, 1 a Ribas, 1 a Abuja.
Hukumar ta ce mutum 35 sun warke zuwa yanzu, 5 sun rasu.
Discussion about this post