An gano cutar coronavirus a jikin wani dan kasar Sierra Leone mai shekaru 37.
Bayyanai sun nuna cewa mutumin ya dawo kasar ne ranar 16 ga watan Maris daga kasar Faransa.
Kafin wannan sanarwa kasar Sierra Leone ce kasar dake yankin Afrika ta Yamma da cutar bai kai gareta ba.
Shugaban kasan Julius Bio ya sanar da haka a talabijin din kasar inda ya cewa tuni an killace wannan mutumi.
Kasar Burundi
Mutane biyu sun kamu da coronavirus a kasar Burundi.
Mutanme biyu da suka kamu suna da masu shekaru 56 da 42 duk sun dawo daga kasar Rwanda ne.
Mutanen na killace a wani otel dake garin Bujumbura.
Ministan kiwon lafiyar kasar ya yi kira ga mutane da su tsaftace muhallinsu da rage yawan shiga taron mutane.
Botswana
Kasar Botswana ta gano coronavirus a jikin wasu mutane uku ranar Litini.
Bincike ya nuna cewa wadannan mutane na da tarihin yin tafiye-tafiye zuwa kasashen waje.
A dalilin haka ne shugaban kasar Mokgweetsi Masisi, ya kafa dokar hana walwala.
Dokar zai fara aiki daga ranar Alhamis karfe 12 na dare.
Tanzania
Coronavirus ta kashe mutum daya a kasar Tanzania.
Mutumin mai shekaru 49 ya rasu a Mlonganzila, Dar es Salam.
A yanzu dai mutum 19 ne ke dauke da cutar a kasar.
Mozambique
A Daren ranar Litini ne shugaban kasar Filipe Nyusi, ya kafa dokar hana walwala.
Dokar zai fara aiki ranar Laraba da karfe 12 na dare zuwa karshen watan Afrilu.
Bisa ga sakamakon binciken Worldometer mutane 5814 ne ke dauke da cutar a Nahiyar Afrika.
A Najeriya mutane 139 ne suka kamu da cutar 8 sun warke sannan biyu sun mutu.
Kasashen Afrika biyar ne suka rage da basu kamu da coronavirus ba a Nahiyar Afrika.
Wadannan kasashe sune Comoros, Lesotho, Malawi, Sao Time, Principe, da Sudan ta Kudu.