CORONAVIRUS: Buhari ya umarci a sallami fursinoni 2600 dake tsare a gidajen kason Najeriya

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumar gidajen yari da ta sallami masu laifi 2600 dake tsare a gidajen kason Najeriya.

Ministan harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola ya bayyana haka ya na mai cewa 70 daga ciki za a sallame su ne daga kurkukun Kuje.

Sauran kuma daga wasu gidajen kason.

Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana cewa majalisar dinkin duniya ta yi kira ga kasashen duniya da su rage cunloson gidajen yari dake kasashen su saboda kauce wa yaduwar cutar coronavirus.

A Najeriya, shugaban hukumar ja’afaru Ahmed ya bayyana cewa babu mai lafi ko daya dake tsare da ya kamu da coronavirus a fadin kasar nan.

Share.

game da Author