Ministan Lafiya Ehinare Osagie ya shaida wa shugabannin majalisar tarayya cewa bashi da masaniya ko ana biyan ma’aikatan lafiya dake aikin coronavirus a kasar nan ka ba a biyan su.
Wannan shine amsar da ya ba shugaban majalisar tarayya Femi Gbajabiamila a lokacin da ya tambayeshi ko yasan nawa ake biyan ma’aikatan lafiya da suka sadaukar da kansu wajen aikin Kula da masu fama da Coronavirus a kasar nan.
Wannan amsa ya yi matukar ba Kakakin Gbajabiamila mamakin gaske ganin cewa gar da gar ace wai ministan kiwon lafiya bai san ko ana biyan maikatan da suka sadakar da rayuwar su ba domin wasu su tsira.
Wani abin takaici da aka bankado game da albashin ma’aikatan lafiya a Najeriya, abin akwai tashin hankali matuka a ciki.
Babban Likita da za a dauka aiki kan karbi albashin naira miliyan 1.7 ne duk shekara. A haka ne zai fara. Haka kuma ma’aikacin jinya da Ungozoma ba su wace naira 360,000 a duk shekara. Haka su ke farawa. da ya kama naira 100,000 da ‘yan kai ga Likitoci, su kuma ma’aikatan jinya, naira 30,000 da ‘yan kai.
Amma kuma dan majalisa a Najeriya na Karbar akalla naira Miliyan 17 duk shekara a matsayin albashi, sanata kuma naira miliyan 24.
Zuwa ranar Juma’a, mutum 305 ne suka kamu da cutar coronavirus a Najeriya, Al sallami sama da mutum 44, mutum 7 sun mutu.
Discussion about this post