CORONAVIRUS: Babu ranar komawar dalibai makarantu tukunna – Gwamnatin Tarayya

0

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa iyayen dalibai da daliban baki daya su yi watsi da wata sanarwa da aka rika watsawa cewa wai za a koma makaranta a kasar nan.

Wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Ilmi ta Tarayya ta fitar, wadda Kakakin Yada Labarai Ben Goong ya sa wa hannu, ya ce iyayen dalibai su yi kaffa-kaffa da labarai na boge da na soki-burutsu.

Yace har yau Gwamnatin Tarayya ba ta aza ranar da dalibai za su koma makaranta ba. Maimakon haka, an shawarci iyaye su bi umarnin gwamnati na daukar dukkan matakan da suka wajaba domin kauce wa kamuwa ko yada cutar Coronavirus a cikin jama’a.

Ya ce sanarwar da aka watsa, wadda a ciki har aka ce Ma’aikatar Harkokin Ilmi ta dora yajin aikin malaman jami’o’i a kan shugabannin jami’o’in, karya ce, kuma takardar sanarwar ta bogi ce karara.

Gwamnatin Tarayya ta bayar da hutun zaman dirshan a gida ga dukkan daliban firamare, sakandare, manyan makarantun sakandare da kuma jami’o’in kasar nan, biyo bayan bullar cutar Coronavirus a Najeriya.

Haka nan kuma ance wa ma’aikatan gwamnatin tarayya daga masu mataki na 10 zuwa 12, duk an ce su ci gaba da zaman gida.

Har yanzu ba a gano maganin cutar coronavirus a duniya ba.

Kasar Amurka ce tafi shiga cikin halin ha’ula’i game da wannan cuta.

Share.

game da Author