CORONAVIRUS: An sallami mutum 11 a asibitin Legas

0

Gwamman Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana wa ‘yan Najeriya cewa yau asibitin da ke kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus ya sallami mutum 11 bayan an yi musu gwaji har sau biyu kuma gwajin ya nuna basu dauke da cutar sun warke.

” Ina so in gaya muku wani abin da zai dadada muku rai yau. Akalla mutum 11 sun warke tas a asibitin Legas. An yi musu gwaji har sau biyu bayan an yi ta kula da su. Yan zu basu dauke da wannan cuta kwata-kwata kuma har an sallame su sun garzaya gidajen su waurin ‘yan uwa.

” Baya ga mutane 11 da aka sallama dama kuma akai 8 da muka sallama a baya. Yanzu mutum 18 kenan a ka sallama.

Gwamna Sanwo-Olu ya yi kira ga mutanen jihar Legas da su kwantar da hankalin su, cewa nan ba dada dadewa ba za a gama da wannan cuta sannan mutane za su ci gaba da harkokin su kamar yadda suka saba.

Wani da aka sallama ya bayyana cewa da farko da aka kawo shi wannan asibiti hankalin shi yayi matukar tashi.

” Da farko dai na dauka ba zai yiwu min ba domin kadaici na fara da shi daga baya kuma na samu abokan zama da malaman asibiti. Kar har dai na saba gashi yanzu har na warke.

” Sai dai kuma dole fa mutum ya rika ankarewa game da wannan cuta. A rika bin dokokin da gwamnati ta gindaya. Shi ne kawai mafita.

” Mu rika nesa da juna, mu daina tarukka. Mu mai da hankali mu bi umarnin gwamnati.”

Share.

game da Author