Saudiyya ta kakaba dokar hana fita ko kofar gida a garuruwa mafi daraja, Makkah da Madina. Wannan wani sabon yunkuri ne domin kokarin dakile fantsamar da cutar Coronavirus ta yi a kasar, inda ya zuwa ranar Alhamis mutum sama da 1,700 suka kamu, kuma ta kashe mutum 16.
Ma’aikatar Al’amurran Cikin Gida ta Saudiyya ta bayyana cewa, an sahale wa masu gudanar da ayyukan lafiya, jami’an tsaro da kuma wasu ‘yan lokuta da aka kebe domin garzayawa a sayo abinci, sannan a hanzarta komawa gida.
Daga nan kuma an tilasta wa kowace mota ta dauki fasinja daya talk Makkah da Madina, domin kauce wa kamuwa da Coronavirus.
Saudiyya wadda kasa ce mai jama’a milyan 30, ta dade da daukar tsauraran matakan gudun kamuwa da cutar Coronavirus. Cikin matakan da ta dauka a baya, ta hana sauka da tashin jirage, an rufe Masallacin Ka’aba, na Madina, takaita dawafi da kuma dakatar dai aikin Umra na shekarar 2020 din nan.
Ranar Laraba kuma Saudiyya ta bayyana cewa kasashen duniya su daina karbar kudade daga masu neman tafiya aikin Hajjin bana. Ta ce kowace kasa ta jira tukuna.
Manyan birane ma irin su Jeddah da Riyadh duk an tsaurara matakan walwala ga jama’a.
Makonni hudu kenan da mahukuntan Saudiyya suka rufe yankin Qatif, inda cutar Coronavirus ta fara bulla daga jikin wasu mabiya Shi’a da suka dawo daga ziyara a Iran.
Saudiyya na sahun farko na kasashen da ke tirsasa a bi doka da karfin-tsiya a duniya.