CORONAVIRUS: An kara wa kotuna hutun makonni biyu

0

Babban Mai Shari’a na Kasa, Muhammad Tanko ya kara wa kotunan kasar nan hurun makonni biyu.

A yau Talata ne hutun da aka ba alkalan kasar nan na zaman killace kai a gida ya kare. An dai ba su hutun tun a ranar 23 Ga Maris zuwa 7 Ga Afrilu.

Wata sanarwa da Cif Jojin na Tarayya ya sa wa hannu da kan sa, ta nuna cewa kowane mai shari’a da ma’aikatan kotu su ci gaba da zama a gida har nan da wasu kwanaki 14, kafin a ga yadda hali ya kama dangane da cutar Coronavirus.

Ya ce kotuna su ci gaba da zama a rufe, masu shari’a su ci gaba da zama a gida, a ci gaba da dakatar da shari’u, sai fa idan bukatar gaggawa ta taso.

Ya umarci dukkan alkalai da ma’aikatan kotu da sauran wadanda abin ya shafa su yada wannan sanarwa.

Coronavirus ta kashe mutum biyar a Najeriya, yayin da ya zuwa ranar Litinin mutum 238 sun kamu da cutar, Amma mutum 33 sun wartsake.

Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta kuma buga labarin cewa ita ma Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya, a wata sanarwa,
Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Muhammad Adamu, ya bayyana cewa daga ranar Litinin din nan, ya umarci dukkan ofisoshin ‘yan sanda cewa kada a rika yawan kulle mutane barkatai, saboda gudun kamuwa da Coronavirus.

Cikin wata takardar da Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Kasa, Frank Mba ya sa wa hannu a madadin Adamu, ya ce daga yanzu duk wanda za a kulle sai an tantance tukunna.

“Na bada umarni kada a sake kama masu kananan laifukan da ba su taka-kara sun karya ba, ana kulle su.

“Daga yanzu saboda gudun Coronavirus, kada a kulle kowa ofishin ‘yan sanda sai dan ta’adda, dan bindiga, dan fashi da makami da kuma wanda ya yi kisa. Sai kuma mai laifin da doka ta hana a bayar da belin sa kadai.”

Adamu ya kara da cewa an kulle dukkan makarantun horas da ‘yan sanda da sauran cibiyoyi, tun bayan da gwamnatin tarayya ta bada sanarwar rufe makarantu.

Daga nan ya sha alwashin cewa jami’an ‘yan sanda za su fara tilasta duk wuraren da gwamnati ta hana budewa su bi doka.

Wannan sanarwa ta nuna irin fargabar da ake yi dangane da cutar Coronavirus a duniya, ko kuma a nan Najeriya.

Sama da mutum milyan daya suka kamu da Coronavirus a duniya, yayin da a kullum cutar sai kisa ta ke yi.

Share.

game da Author