Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari ta wallafa littafin zane-zanen wayar da kan hada-hadar kudade

0

Cibiyar Hada-hadar Hannayen jari ta Najeriya (Nigeria Stock Exchange, NSE), ta wallafa wani littafi mai dauke ta bayanai a cikin zane-zane dalla-dalla a kan yadda za a wayar wa mutane kai su ilmantu da muhimmancin hada-hada da tu’ammali da kudade ta hanyar zamani.

Littafin wanda shi ne irin sa ba farko, mai suna StockTown, akwai bugaggen sa, sannan kuma akwai shi a intanet, wanda za a iya kwafa a http://www.nsestocktown.com.

Littafin an yi matukar kokari a cikin sa, inda aka yi amfani da dabarun ilmantarwa a sigar zane-zane, aka nuna wa jama’a manya da kanana muhimmancin adani, tattalin kudade da kuma zuba jari.

Da ya ke bayani game da littafin, Shugaban NSE, Oscar Onyeama, ya ce basirar kirkiro littafin dadaddiyar aba ce a NSE, domin a nuna wa mutum ko wasu jama’a muhimmancin inganta rayuwar su ta hanyar adani da tattali da kuma zuba jari.

NSE a kowace shekara ta na gudanar da tsare-tsaren da ta ke ilmatlntar da yara, inda a 2019 ta samu nasarar isar da sakonnin ta ga yara kimamin 60,000 a cikin shirin wanda ta gudanar a cikin mako daya.

Cikin wadanda ta ke maida hankali a kan su, akwai yara ‘yan sakandare masu yawa da kuma daliban jami’a da dama a kasar nan.

Share.

game da Author