Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sassauta dokar Hana walwala a jihohin Legas da Ogun da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Daga ranar 4 ga watan Mayu, za a ci gaba da walwala tun daga karfe 9 na safe zuwa karfe 8 na dare, daga nan kuma za a shiga kulle sai safiyar gobe.
Hakan na nuni cewa shugaban kasa ya kara wa jihohin har da Abuja ‘Zaman Gida Dole’ na mako guda kenan.
Buhari ya Kara da cewa gwamnatin tarayya zata tallafa wa gwamnatin Kano domin kawo karshen matsalolin da suke fama da su.
A bisa haka Buhari ya ba da umarnin garkame Kano na tsawon kwanaki 14 daga ranar Talata.
Daga nan sai yayi Kira ga gwamnatocin jihohi su ci gaba da kare mutanen jihar su da samar musu da tallafi.
Discussion about this post