Boko Haram sun kashe matafiya bakwai, sun banka wa tirelar buhunan wake wuta

0

Ranar Lahadin nan da dare Boko Haram suka yi wa matafiya kwanton-bauna suka bindige mutum bakwai, kuma suka banka wa tirela mai dauke da buhunan wake wuta.

Lamarin ya faru kusa da garin Auno, da ke kilomita 20 kusa da Maiduguri, a kan hangar Damaturu.

Wanda ya gani da idon sa ya tabbatar da cewa sun iso kusa da kauyen auno, “sai mu ka ci karo da gawarwakin mutane a kan titi.

“Sannan kuma na ga motoci biyu da aka banka wa wuta. Daya motar Hulux ce, dayar kuma babbar mota ce wadda aka lodo wa wake za ta Maiduguri. Har lokacin da mu ka isa wurin da safe, motar da ke dauke da waken ba ta daina cin wuta ba.”

Jami’in kungiyar Motocin Surufi na Maiduguri (NURTW), Malam Ali ya shaida wa wakilin mu cewa ba su da cikakken bayanin yawan mutanen da aka kashe.

An kai wannan hari kwana kadan bayan Babban Jafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya Tukur Buratai ya yi shelar komawa Barno domin jan rundunar da za ta karasa Boko Haram kurmus.

Boko Haram sun sha tare matafiya kusa da Auno. Ana ganin cewa su na samun damar kai harin ne ta hanyar biyowa cikin kwararon wani burtali da ke kusa da garin Auno.

Idan ba a manta ba, Jihar Barno ta saka dokar zirga-zirga a fadin titinan jihar, banda na Maiduguri zuwa Damaturu.

Dukkan kokarin jin ta bakin Kakakin Yada Labarai na Sojojin Najeriya Sagir Musa, ya ci tura, domin bai amsa kira ko maida amsa ba.

Jihohin Barno da Yobe da wasu sassa na Adamawa na ci gaba da fuskantar hare-hare daga Boko Haram.

Share.

game da Author