Binciken da ake yi a Kano zai bayyana musabbabin yawan mace-macen da ake yi -Fadar Shugaban Kasa

0

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa tambayoyin da ake wa jama’a, ana jin ta bakin su a Kano, zai bayyana musabbabin yawan mace-macen da ake yi a Kano, kamar yadda fadar ta bayyana.

An samu yawan mace-mace a Kano cikin ‘yan kwanaki, abin da aka rika cewa cutar Coronavirus ce ta kashe su.

Sai dai kuma dukkan su ba a tabbatar ba, saboda ba a auna su ko gwada su an samu cutar a jikim su ba, kafin a binne gawarwakin su.

Kakakin Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ne ya ce, “ana nan ana ci gaba da yi wa jama’a tambayoyin domin a gano hakikanin musabbabin mace-macen.”

Haka ya rubuta a cikin wata takarda da ya aiko wa PREMIUM TIMES.

Yadda Ake Tambayoyin: Irin wadannan tambayoyin su na nufin yadda masana kiwon lafiya za su bi jama’a su na yi musu tambayoyi kan wasu alamomin da mamaci ya rika nunawa a lokacin da ba shi da lafiya.

Za a rika bin mutanen da ke kusa wato makusantan mamaci su na bada bayanin irin raashin lafiyar da ya rika fama da ita da kuma irin magungunan da ya rika sha, amma ba su yi masa amfani kafin ya mutu.

Daga nan idan aka tattara wadannan bayanai, su ne likitoci za su yi amfani da su domin tantance musabbabin mutuwar mamacin.

Garba Shehu ya shawarci ‘yan Najeriya su amince da sakamakon da za a fito da shi dangane da wadannan yawan mamace a Kano.

Hukumar NCDC ta fitar da bayanin cewa Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi bayanin cewa a yanzu ne cutar ke kara makasura a Afrika, bayan ta rigaya ta gama makasura a sauran sassa na duniya.

Kano ce ta uku a Najeriya a jerin jihohin da ke da yawan masu dauke da cutar Coronavirus a Najeriya. Lagos ce ta daya sai Babban Birnin Tarayya Abuja na biyu.

Wakilin PREMIUM TIMES HAUSA da ke Kano ya lura har zuwa lokacin da ake rubuta wannan labari, jama’a da dama na ci gaba da mutuwa a kullum.

Da ya ke dokar zaman gida ake yi a Kano, ana gane yawan mace-macen da ake yi ta hanyoyi hudu.

Hanya ta farko ita ce masu watsa labarin mutuwar da aka yi a unguwar su tare da sunan mamacin, musamman a shafukan soshiyal midiya, musamman idan sananne ne, ko kuma wani na sa sananne ne.

Hanya ta biyu kuma ita ce yadda masu gidaje kusa da makabartu ke ganin yadda ake yawan shiga da gawarwaki a cikin makabartu babu kakkautawa.

Hanya ta uku kuma ita ce yawan kiran ‘yan uwa da abokan arzikin mamaci wadanda ke zaune a wasu unguwanni daban, ana fada musu zance ko sanarwar wanda aka yi rashi.

Hanya ta hudu kuma ita ce bayanan da masu gadin makabartu ke yi wa jama’a, su na shaida musu yawan gawarwakin da aka rufe a makabartun.

Hanya ta biyar kuma ita ce yadda masu kai gawarwaki a makabartu kan lisaafa ko su dauko hotunan sabbin kaburburan da aka rufe gawarwaki a ranar da suka kai gawar da su ma suka binne.

Share.

game da Author