Dan tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar, Mohammed Abubakar ya bayyana warke daga cutar Coronavirus da yayi fama da na tsawon kwanaki 40.
” Yau ne aka yi min gwaji na biyu da ya nuna bani dauke da cutar coronavirus. Yanzu haka ana shirin Sallama na ne, Insaha Allahu zan isa gida da yamman yau.
Mohammed Atiku ya killace kan sa bayan an tabbatar masa da kamuwa da cutar Coronavirus ranar 19 ga watan Maris.
Sai dai dama hukumar NCDC ba su fadin sunayen wadanda uka kamu ko warkewa sai dai mutum ko wani nasa ya fadi da kansa.
Jihar Adamawa ta samu wanda ya kamu da cutar a karaon farko a makon da ya gabata. A Najeriya kuma a mutum sama da dubu daya da dari biyu ne suka kamu da cutar. Jihar Legas ce ke kan gaba a yawan wadanda suka kamu da cutar.