BAUCHI: Yadda masu garkuwa suka kashe min da, duk da na biya miliyoyin naira kudin fansa – Likita Rilwan Sadiq

0

Wani kwararren likita da ke aiki a asibitin koyarwa na jami’ar Abubakar Tafawa Balewa, dake Bauchi ya bayyana yadda wasu mahara da basu da imani suka amshe masa naira miliya 4.5 kudin fansan dan sa Abubakar Sadiq da suka yi garkuwa da sannan suka kashe shi.

Shi dai Abubakar Sadiq ya gamu da ajalin sa ne bayan masu garkuwa sun arce dashi a kofar gidan su dake titin Gombe, a garin Ningi, jihar Bauchi.

Mahaifin Sadiq ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa masu garkuwan sun kira shi, suka sanar dashi abinda suka yi da halin da dan sa ke ciki. Sannan suka bukaci ya kawo naira miliyan 3 kudin fansa.

Rilwan ya ce ya fara aika musu da naira miliyan 2.5 a karon farko. hakan bai ishe su ba. Daga baya suka ki sakin wannan yaro. suka yi ta neman yayi musu kari.

” Ni kuma na yi kamar yadda suke so. Har dai na kai musu naira miliyan 4.5. Kuma duk da haka suka ci gaba da tambayan kari. Haka na yi ta fama da su daga baya dai na ce su yi wa Allah su saka min da.

Rilwan ya ce a inda suka tsinci gawan dan, wani kango ne dake kusa da unguwar su. sannan kuma yana da yakinin cewa wadanda suka aikata wannan abu sun san shi kuma shige da ficen iyalan sa, wato makusanta ne.

‘Yan sandan jihar Bauchi sun bayyana cewa sun kama wasu mutane biyu dake zaton suna da hannu a aikata wannan abu.

Share.

game da Author