BASHIN IMF: Najeriya za ta biya kudin cikin shekaru biyar

0

Bashin zunzurutun kudade har dala bilyan 3.4 da Najeriya za ta ciwo a Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF), za ta biya ne cikin shekaru biyar.

Najeriya ta bayyana cewa za ta ciwo bashin ne domin amfani da kudaden wajen sassauta wa al’ummar kasar kuncin da aka shiga sakamakon barkewar cutar Coronavirus a Najeriya da ma duniya baki daya.

Bashin kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar, an kakaba wa Najeriya ka’idojin karba da kuma biyan bashin.

A ranar Talata da ta gabata ce Shugabannin IMF suka rattaba hannun amincewa a bai wa Najeriya bashin dala bilyan 3.4.

PREMIUM TIMES ta tuntubi wakilin Bankin IMF a Najeriya, mai suna Amine Mati, wanda ya tabbatar wa jaridar da cewa ba haka sakaka kadai aka bai wa Najeriya bashin ba, sai da aka kakaba wasu sharudda.

Da ta ke yi sa PREMIUM TIMES karin hasken sharuddan, wata jami’ar IMF a Najeriya mai suna Laraba Bonet, ta tabbatar da cewa an bai wa Najeriya wa’adin biyan kudin a cikin shekaru biyan nan gaba.

Sannan kuma an dora ma ta kudin ruwa na kashi 1% bisa 100% na kudin.

Ranar Laraba PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin cewa Shugaba Muhamadu Buhari zai rakito bashin dala bilyan 3.4 daga IMF, domin daukin gaggawa.

Jaridar nan ta ce Bankin Bada Lamuni na Duniya (IMF) ya amince da rokon da Gwamnatin Najeriya ta yi, na neman bashin dala bilyan 3.4, domin gaggauta ayyukan farfado da tattalin arziki kasa.

Manyan Daraktocin Bankin IMF ne suka amince da rokon wannan bashi d Najeriya ta nemi a ba ta da gaggawa, domin yayyafa wa tattalin arzikin kasar ruwa daga sumar da cutar Coronavirus ta sa ya yi.

Wannan ne makudan kudade mafi yawa da Bankin IMF ya bai wa wata kasar Afrika lamuni tun bayan barkewar Coronavirus.

Baya-bayan nan IMF ya bai wa kasar Ghana lamunin dala bilyan 1.

Ranar 6 Ga Afrilu ne Ministar Harkokin Kudade, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed ta ce Najeriya ta kaddamar da gidauniyar neman yadda za ta harjadp naira bilyan 500 domin amfani da kudin a buga wa tayoyin motar tattalin arzikin Najeriya, wadanda suka sacce tun bayan barkewar cutar Coronavirus.

Kokarin hakan ne ya sa Najeriya ta garzaya garzayawa har Bankin IMF domin neman rufin asiri.

Daga nan Zainab ta ce sauran hanyoyin samun kudaden sun hada da bashin dala bilyan 2.5 daga Bankin Duniya sai kuma wani bashin na dala bilyan 1 daga Bankin Bunkasa Kasashen Afrika (AfDB).

Zainab ta ce za a yi amfani da bashin IMF da na Bankin Duniya domin a yi cike gibin matsalar kudi da ta rufta wa Najeriya, tun bayan da asusun kudin wajen kasa ya kusa yin karkaf.

Sannan kuma da kudaden ne idan an karbo za a talmalmala a gudanar da wasu ayyukan kasafin kudi, ganin cewa hakan ne kadai mafiya, tunda farashin danyen mai ya fadi warwas, kamar farashin karan taba sigari a duniya.

Share.

game da Author