Kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar cutar Covid-19 ta bayyana cewa ba za a iya kamuwa da cutar Covid-19 ba ta hanyar Jima’i ba.
kwamitin ta ce masana kimiya ba su samu tabbacin ko ana iya yada cutar ta hanyar jima’i ba domin har yanzu ana gudanar da bincike akan cutar.
Sani Aliyu ya Sanar da haka bayan zaman da kwamitin ta yi ranar Laraba a Abuja.
Idan ba a manta ba ministan Kiwon Lafiya ya bayyana a kwanakin baya cewa akwai yiwuwar za a iya kamuwa da cutar ta hanyar saduwa da juna.
Masana kimiya sun tabbatar cewa jima’i baya hadassa cutar a jikin mutu amma ana iya kamuwa da cutar ta hanyar yin wasa kafin a yi jima’i.
Wata likita a kasar Birtaniya mai suna Jessica Justman ta bayyana wa gidan jaridar ‘Guardian UK’ cewa mutum zai kamu da cutar idan ya kusanci mai dauke da ita sai dai kamuwa da cutar ta hanyar jima’i ne babu wani tabbaci a kai.
Bayan haka Aliyu ya ce kwamitin na fama da matsaloli da suka shafi aiyukka da wuraren gwajin cutar coronavirus a kasar nan.
A ranar Laraba ne Hukumar NCDC ta Najeriya ta sanar da karin wadanda suka kamu da cutar coronavirus a kasar nan.
A bayanan da NCDC ta fitar Legas ta samu karin mutum 74, Abuja 1, Katsina 5, Ogun 4, Delta 2, Edo 2, Kwara 1, Oyo 1, Adamawa 1.
Yanzu mutum 873 kenan suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 197 sun warke, 28 sun mutu.
A sakamakon gwajin da aka fitar Jihar Legas ce kan gaba wajen yawn wadanda suka kamu da cutar, Sai kuma babban birnin Najeriya, Abuja.
Jihar Kano ma ta ci gaba da kawo maki mai yawa da har yanzu itace jiha ta uku da tafi yawan wadanda suka kamu.
Jihar Adamawa ma ta samu mutum daya cikin wadanda aka fidda a sakamakon gwajin ranar Laraba.