Sarkin Musulmi sultan Abubakar Sa’ad ya sanar cewa ba za ayi sallar Taraweeh, Tafsirin Ramadan, da I’tikafi da aka saba yi duk watan Ramadan ba.
Sarkin Musulmi ya bayyana haka ne bayan ganawa da kwamitin fatwa tayi ta yanar gizo ranar litini.
Sultan Abubakar ya ce hakan ya hallat a musulunci kuma ma annabin SAW, ya kwadaitar da a kiyaye daga annoba ko wacce iri ce.
A dalilin haka kwamitin ta yanke cewa a Ramadan din bana ta dakatar da tafsirin Azumin da ka saba yi, kuma babu sallar taraweeh da kuma ibadar i’itikafi
Sultan ya ce idan ya kama mutum zai iya yin I’tikafi a gida.
” Idan har za a iya dakatar da sallar juma’a duk muhimmancin ta a addini, haka za a yi hakuri a dakatar da sauran salloli domin a kare mutane daga kamuwa da cutar.
Sannan kuma ya hori mutane da su bi doka kamar yadda aka kafa su kuma a ci gaba da addu’o’i Allah ya kawo mana karshen wannan jarabawa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito bayannan taron kamar yadda ya gudana.
Discussion about this post