Gwamnatin Barno ta bayyana cewa ba coronavirus bace ta kashe marigayi Sarkin Bama, Kyari Ibn Umar Elkanemi.
Kwamishinan yada labarai na jihar Barno Babakura Jato ya bayyana cewa marigayi Sarkin Bama ya rasu a gidan sa dake Maiduguri.
Kwamishina Jato ya kara da cewa Marigayi Kyari Ibn Elkanemi ya dade baya garin Bama, tun bayan kwace garin Bama da Boko Haram Suka yi. Haka kuma ko da aka kwato garin, bai koma ba.
A karshe kwamishina Jato ya ce babu abin da ya hada rasuwar maimartaba Sarkin Bama, da cutar Coronavirus. Ya bayyana haka a wajen ganawar kwamitin dakile yaduwar coronavirus na jihar Barno.
Discussion about this post