Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana cewa jihar ba za ta lamunta wa mahara da ‘yan ta’adda ba a jihar.
Aruwan ya bayyana cewa jihar ba za ta tattauna da mahara ba yana mai cewa wanda yayi za a yi masa ne kawai, babu sassauci.
Kwamishina Aruwan ya kara da cewa gwamnati za ta ci gaba da samarwa mutanen jihar tsaro yadda ya kamata a ko ina suke a fadin jihar.
Aruwan yayi wadannan kalamai ne a taron ganawa da yayi da sabon kwamanda rundunar Operation Safe Haven dake aiki a Jihar Filato da yankunan jihar Kaduna da aka yi a garin Kafanchan.
” Ba za mu sa ido mu bari wasu suna yi mana shishshigi a ayyukan tsaron jihar Kaduna ba ta hanyar yi mana katsalandan. Tsaron mutanen jihar Kaduna shine muka sa a gaba kuma abinda za mu ci gaba da yi kenan.
” Duk da ‘yan matsalolin tsaro da muka samu a wasu lokuttan, dakarun mu sun samu nasarori da dama kan mahara da ‘yan bindiga. Sun ragargaza su kuma an kwato makamai masu yawa a samame da farmaki da aka kai wa mahara a jihar.
” Muna godewa kwamandojin da suka wuce a baya da muka yi aiki da su kuma muna tabbatar wa sabon kwamanda cewa zai samu duk hadin kan da zai bukata daga gwamnati wajen aikin sa.
A karshe sabon kwamanda Manjo Janar Chukwuma Okonkwo, ya tabbatar wa gwamnatin jihar cewa dakarun sa za suyi aiki tukuru wajen samar da tsaro a jihar.
Discussion about this post