Tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya sake furta cewa ba shi da ko sisi kuma bai sayi ko fegi ya boye a kasashen waje ba.
Haka Jonathan ya sake nanatawa a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kakakin Yada Labarai na Jonathan, Ikechukwu Eze ne ya fitar da sanarwar a madadin sa, biyo bayan wasu wasiku da gwamnatin Najeriya ta tut-tura wa bankuna a Amurka, inda ta rika tambayar su cewa idan Jonathan da matar sa Patience sun ajiye kudade a can, to gwamnatin ta Najeriya ta na so ta sani.
“An jawo hankalin mu dangane da wani rahoto da kafafen yada labarai na waje suka watsa cewa Gwamnatin Tarayya ta baza komar farautar asusun bankunan da Tsahon Shugaban Kasa, Goodluck Jonathan da uwargidan sa, Patience Jonathan suka kimshe kudade a Amurka.
“Mun hakkake cewa Gwamnatin Tarayya ba ta tuntubi Jonathan ko matar sa Patience ba kafin ta aika da wasikun neman asusun ajiyar na su. Da sun tuntube su, to da gwamnatin ba ta bata lokacin rubuta wasikun neman ko sun yi ajiyar kudaden ba. Saboda ba za su taba samun abu inda ba a ajiye ba.
“Mu na kuma kara tunatar da Gwamnatin Tarayya bayanin da Jonathan ya yi a ranar 5 ga Maris, 2014, lokacin da ya ke rantsar da Ministoci, inda ya ce, “ni mutum ne mai biyayya ga Najeriya. Ban ajiye ko sisi a wata kasa ba, kuma ba ni da ko fegi balle gidan kai na a wata kasa.”
Sanarwar dai ta kara da cewa daga lokacin da Jonathan ya yi furicin zuwa yau, babu wani abu da ya canja a bangaren Jonathan. Wato har yau ba shi da kudi ajiye ko wasu kadarori a wata kasa.
Kafar yada labarai ta Bloomberg ta ruwaito cewa Gwamnatin Najeriya ta roki Bangaren Shari’ar Amurka, inda ta nemi a ba ta izni ta ai ka sa wasu bankuna 10 takardar neman inda Jonathan da matar sa suka boye kudi a Amurka, idan har sun boye.
An ce Najeriya na ta hakilon neman hanyar da za a soke mata diyyar haddin biyan makudan kudade daga harkallar dala bilyan 9.6 na kamfanin P& ID.