Wasu masu fama da ciwon Asthma a Jihar Bauchi sun koka dangane da yadda ake kyamatar su, ana yi musu kallon masu dauke da cutar Coronavirus.
A zantawar su da manema labarai a Bauchi, wadanda aka yi hirar da su sun ce saboda babba daga cikin alamomin mai ciwon Asthma shi ne wahalar yin numfashi, to sai ake musu kallon cewa Coronavirus ce ke damun su.
Dalilin haka kuwa a cewar su shi ne saboda likitoci sun bayar da fatawar cewa kasa yin numfashi a cikin sauki wata alama ce ta cutar Coronavirus, ko da ba a kai ga auna maras lafiya ba.
Sun kara da cewa ko wani tari ko kakari suka yi a cikin jama’a, sai a rika tsana da tsangwama da kyamar su.
Sun ce a wasu wurare ma idan suka yi kokarin bayyana wa jama’a bambancin tarin Asthma, sai a rika watsewa a guje daga wurin su.
Wata mai fama da ciwon asthma mai suna Hadiza Usman, ta ce abin haushi da takaici ta kai a yanzu har makwautan ta wadanda suka san ta na fama da ciwon tarin asthma tun kafin bullar Coronavirus, a yanzu kyarar ta su ke yi, kuma su na nuna jahilcin cewa cutar Coronavirus ce wai ke damun ta.
“Tsoron cutar Coronavirus ya sa ko ciwon mai Asthma ya tashi, da ya fara tari hatta wadanda suka san ka da ciwon tun tuni, sai su fara shan jinin jikin su, su na baya-baya da kai.”
“Kai ‘yan uwan ka da ka ke takama da su, sai su tsangwame ka, su yi maka kallon mai dauke da wata annoba. Saboda na san wani mai fama da asthma, wanda dan uwan sa ya nemi ya kira masa jami’an Hukumar Kula da Cututtuka (NCDC), domin su auna shi su gano shin Asthma ce ke damun sa ko kuwa Coronavirus?”
Umar Mohammed da Umaru Galadima duk sun bayyana yadda aka rika kyamatar su ana yi musu kallon masu dauke da cutar Coronavirus.
“Sai biyu ana wulakanta ni a cikin jama’a. Na farko na je cirar kudi a banki, ina kan layi, sai asthma ta ta tashi. Na fita daga layi, na dan yi tari na na dawo. Amma sai na ci gaba. Kawai sai na ga jama’a sun watse daga kusa da ni, an ki tsayawa a inda na ke tsaye.
“Kai sai da ta kai har wani kwastoma ya kira jami’in tsaro ya nuna ni. Duk da kokarin da na yi wajen yin musu bayani, duk ban gamsar da su ba.” Inji Umar Mohammed.
Alamomin cutar Asthma dai su ne wahalar yin numfashi, ciwon kirji da kuma tari.
Yayin da ita kuwa Coronavirus, kasa yin numfashi, zarrabi, tari da zubar majina da sauran su.
Discussion about this post