An yiwa kamfanin shinkafa na Tiamin kagen ta’azzara ciwon coronavirus

0

Shugaban kamfanin sarrafa shinkafa mai suna TIAMIN RICE LIMITED ranar Lahadi ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta umarce shi da ya kulle
masana’antar ta sa kan zargin gurbatacciyar iskar da kamfanin ke fitarwa, inda ta ce iskar ce ke ta’azzara rashin lafiyar ma su fama da
cutar coronavirus a jihar.

A tuna cewa a jawabin da ya yi wa ya’n kasa, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya cire duk wasu kamfanunuwa da su ke yi da sarrafa abinci daga doka domin a rage radadin cutar a kan ya’n kasa a kuma tabbatar da yalwar abinci.

A martanin sa kan umarnin rufewar, Mataimakin Babban Manajan kamfanin, Aliyu Ibrahim ya ce zargin na gwamnatin ba shi da tushe, musamman ma
duba da cewa nisan sama da kilomita 20 ne tsakanin kamfanin da cibiyar killace masu cutar coronavirus din da ke Filin Wasan Kwallon
kafa na Sani Abacha.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Mataimakin Babban Manajan ya nuna cewa a kwai masana’antun sarrafa shinkafa kusan 30 da su ke aiki a jihar, in da ya yi mamakin dalilin da ya sanya kamfanin sa ne kawai ya tsonewa gwamnatin ido.

Ya bayyana cewa shugabancin kamfanin ya samu takardar da gwamnatin ta aiko ne ta hannun Ma’aikatar Kula da Muhalli ta Jiha a ranar 18 ga
Afrilu, 2020.

Ya ce “Mun samu sakon matakin da gwamnati ta dauka ta mu rufe kamfanin mu ne a wata “Sanarwa ta Rufewa” ran 18 ga Afrilu, 2020. Inda ta kawo wani zargi mara tushe cewa muna fitar da gurbatacciyar iska wacce take ta’azzara jikin masu fama dacutar coronavirus.

“Sanarwar ta kara da cewa gwamnati ta dauki matakin ne duba da korafe-korafen da ta samu cewa muna fitar da gurbatacciyar iska da har
ta ta’azzara cutar coronavirus,”

“Maganar gaskiya, akwai kusan masana’antun sarrafa shinkafa kusan 30 da su ke aiki a jihar nan, amma TIAMIN RICE LIMITED ne kadai umarnin ya shafa, duk da nisan kamfanin na sama da kilomita 20 daga cibiyar killace masu cutar da ke filin wasan kwallon kafa na Sani Abacha,” in ji shi.

Mallam Ibrahim ya yi takaicin cewa rufe kamfanin zai haifar da gagarumar illa a kan tattalin arzikin kasa musamman ma na Jihar Kano,
inda ya ce “zai lalata tattalin arzikin jihar mu kuma zai jefa al’umma cikin yunwa.”

Yayin da ya ke fafutukar warware matsalar ta hanyar maslaha, kamfanin ya tabbatarwa da abokan harkar sa cewa kada su firgita a kan matsalar
wacce shugabancin ya suffanta ta da cewa ba mai dorewa ba ce.

“Ina mai alfahari da sanar da ku abokan harkar mu masu girma cewa masana’antar mu da za ta rika sarrafa shinakafa mai yawan ton 600 da
ke Jihar Bauchi na daf da fara aiki.

“Ina mai tabbatar muku da cewa nan ba da dadewa ba komai zai yi dai-dai da yardar Allah, kawai dai mu ci gaba da yin imani da shi.
Sannan kuma ma’aikatan lafiyar mu na iya bakin kokarin su a wannan mawuyacin hali da mu ka tsinci kan mu,” in ji sanarwar.

Share.

game da Author