An yi jana’izar marigayi Abba Kyari a Abuja

0

A safiyar Asabar ne aka kawo gawar marigayi shugaban fadar gwamnatin Tarayya, Abba Kyari daga Legas zuwa Abuja domin a rufe shi.

An rufe shi a makabartar Gudu da ke Abuja da misalin 11da rabi.

Fadar shugaban Kasa ta bayyana cewa babu taron zamammakoki da za ayi, kowa ya yi wa marigari Abba Kyari Addu’a a duk Inda yake saboda irin halin da ake ciki yanzu.

Abba Kyari ya rasu ranar Juma’a a asibiti dake Legas bayan yayi fama da Coronavirus.

Maitaimaka wa shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya bayyana haka a madadin gwamnatin Tarayya.

Adesina ya ce Abba Kyari ya rasu ranar Juma’a a asibiti a Legas.

Idan ba a manta ba a ranar 29 ga watan Maris, Abba Kyari ya sanar da cewa za a maida shi asibiti a Legas domin a ci gaba da duba shi.

Sai dai ko a lokacin bai fadi ko wani asibiti bane za a kwantar dashi.

PREMIUM TIMES ta gano wani asibiti mai zaman kan sa dake Ikoyi a Legas aka kwantar da Marigayi Abba Kyari.

Majiya mai karfi daga asibitin ya shaida wa jaridar cewa Marigayi Abba Kyari yayi fama da wannan cuta tun bayan da aka kwantar dashi a asibitin.

Majiyar ya ce, a wasu lokuttan ma har wasu manyan asibitoci aka rika Kai shi ana yi masa gwaje-gwaje.

Ranar Juma’a, hukumar NCDC ta bayyana rasuwar wasu mutum hudu daga cutar coronavirus da bata da magani har yanzu ana gani ciki har da marigayi Abba Kyari.

Sannan kuma mutum sama da 490 suka kamu da cutar a Najeriya.

Jihar Kano da bata wuce mako daya da bayyana mutum na farko da ya kamu da cutar ba ta zarce jihohin kasarnan a yawan wadanda suka kamu.

Yanzu ita ce jiha ta uku dake da yawan wadanda suka kamu da cutar a Najeriya bayan Legas dake da mutum sama da 200 kwance.

Share.

game da Author