Jim kadan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sanarwar kara kulle Abuja na tsawon wasu karin makonni biyu, kamfanin StarTimes, wanda kashi 70% mallakar ‘yan Chana ne, sun bude hedikwatar su da ke Abuja, da ma sauran ofishin su. Haka dai binciken PREMIUM ya tabbatar.
Wannan umarnin komawa aiki da aka yi sa ma’aikatan StarTimes sun rika korafi, guda-guni da nuna fargaba, domin a cewar su, dokar farko ta makonni biyu, duk a gida suka gudanar da ayyukan su, kuma sun yi kamar yadda ya kamata.
Sai dai kuma wani mai magana da yawun kanfanin, ya ce sun fito domin alkadarin harkokin kasuwancin na su na neman durkushewa, saboda gwamnati ba ta ba su wani tallafi.
PREMIUM TIMES ta gano cewa dokar zaman gida ta farko dai StarTimes ta bar ma’aikatan ta sun rika gudanar da ayyukan su daga gidajen su.
PREMIUM TIMES ta gano cewa kafin Shugaba Buhari ya yi jawabin sa, sai mahukuntan StarTimes suka rika sakonni ga ma’aikatan su ta e-mel cewa kowa ya fito aiki a ranar Litinin.
Bayan Buhari ya yi jawabi, inda har ya kara wa’adin kwanaki 14, sai aka sake tura wa ma’aikatan StarTimes sako cewa su yi watsi da umarnin Buhari, kowa ya ya fito aiki kawai.
An lissafa sunayen ma’aikatan da aka umarta su fito, su 45 wurin aiki, a kamfanin wanda hadin guiwa ne da Gidan Talbinin na NTA.
Lauyan kamfanin mai suna Nwankwo Amaechi, ya ce sun bi umarni daga farko sun zauna a gida, amma kuma a yanzu sun fahimci masu kama tashohin talbijin na yi musu korafe-korafe. Sannan kuma ya ce jawabin shugaban kasa na farko ya nuna za su iya fitowa su yi aiki.
Amma kuma jawabin ya nuna cewa sai kafar yada labarai wadda ta bada kwakwarar shaidar cewa ma’aikatan su ba za su iya aiki a gida ba.