Allah yaji kan Sarki Jere, Sa’ad Usman – Ta’a ziyyar Buhari

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga iyalan maragayi Sa’ad Usman, Sarkin Jere.

A takarda da mai taimakawa shugaban kasa kan harkar yada Labarai Femi Adeshina, ya fitar ranar Alhamis, Buhari ya yi wa marigayi Sa’ada addu’ar Allah ya ji kan sa.

Marigayi Sa’ad Usman ya rike sakataren gwamnatin jihar Kaduna a lokacin gwamnatin Marigayi Dabo Lere kuma shine mijin tsohuwar ministan kudi, Nenadi Usman.

Share.

game da Author