Allah ya ji kan Abba Kyari – Aisha Buhari

0

Uwargidan shugaba Kasa Muhammadu Buhari, Aisha Buhari ta mika ta’aziyyar ta ga iyalai da ‘yan uwan marigayi Abba Kyari.

Aisha ta yi addu’ar Allah ya gafarta masa.

Idan ba a manta ba, Aisha bata ga maciji da marigayi Abba Kyari, inda a lokutta da dama ta rika fitowa ta na sukan sa da Mamman Daura, cewa sun kanannade maigidanta sun hana shi yin abin da ya kamata.

Abba Kyari ya rasu ranar Juma’a a Asibiti dake Legas.

An yi jana’izan sa a Abuja ranar Asabar.

Abba Kyari ya yi fama da cutar coronavirus da ya kamu da tun bayan dawowarsa daga kasar Jamus, a karshen watan Maris.

Tun a lokacin ya killace kan sa inda daga baya aka maida shi wani asibiti mai zaman kansa a Legas.

Marigayi Abba Kyari yayi fama da cutar inda har an rika canja mishi asibiti ko a Legas din domin yi masa gwaje-gwaje.

Allah ya ji kansa.

Share.

game da Author