Akwai yiwuwar a yi fama da karancin abinci, idan ba a samun hadin kan mutane wajen fallasa ayyukan mahara ba – Gwamnatin Kaduna

0

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin gida, Samuel Aruwan ya yi kira da mazauna yankunan da mahara suka addaba cewa dole sai an hada kai da jami’an tsaro don asamu nasarar dakile ayyukan su.

Ya ce za a samu nasarar haka ne idan mazauna suna ba jami’an tsaro hadin kai a ayyukan su.

Aruwan yayi takanas-ta-kano zuwa garin Sabon Birni tare da kwamandojin sojojin Najeriya inda suka gana da sarakuna, dagatai da masu unguwannin kauyukan dake wannan yanki domin tattauna hanyoyin da za abi wajen karya lokon mahara da suka addabi musamman Sabon Birni da kewaye.

Sabon Birni da kauyukan dake kewaye da wannan gari na fama da auyukan ‘yan ta’adda. Mazauna garuruwan dake kewaye da garin su koka kan yadda hare-haren mahara ya jefa manoma cikin hali ha’ulai.

Babban kiran da kwamishina Aruwan yayi ga mutanen kauyukan shine mutane su rika ba jami’an tsaro goyon baya wajen samar musu da bayanai da zai taimaka wajen fatattakar wadannan muggan batagari.

” Taimakawa jami’an tsaro da bayanai zai taimaka matuka, kuma ma dai hakan shine ya fi dacewa domin a iya kau da su. Rashin samun irin wannan hadin kai zai sa ayi fama da karancin abinci domin manoma ba za su iya zuwa gona ba.

A jawabin sa Birgediya Abai ya bayyana cewa hadin kai tsakanin jami’an tsaro da mazauna garuruwan zai taimaka matuka wajen kawo karshen ta’addanci a yankunan.

Mahukuntan sun gana da mutanen mazauna Kauyukan Sabon Birni, Ifira, Rubu, Riyawa, Afaka Tsoho da Fauta.

Share.

game da Author