Abin da ya hana Gwamnatin Tarayya fara daukar ma’aikata a kananan hukumomi 774 – Minista

0

Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ya bayyana dalilin da ya sa har yanzu ba a fara daukar ma’aikata a fadin kananan hukumomi 774 na kasar nan ba.

Shugaba Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin a dauki ma’aikata a kowace Karamar Hukumar a fadin kasar nan.

Sai dai kuma a lokacin da ya ke wa manema labarai bayani a taron Kwamitin Yaki da Coronavirus, Minista Aregbesola ya ce hakan bai yiwu ba, saboda dokar killace kai a cikin gida da kuma hana zirga -zirga da aka kakaba.

Ya ce yawancin jami’an da za su aikin duk su na zaune gida a halin yanzu. Saboda haka a wannan mawuyacin hali da ake ciki, babu wadanda za su fito su yi wannan aikin.

“Matasa su kwantar da hankulan su. Za a ci gaba da aiwatar da wannan umarni na Shugaban Kasa da zaran an saki dokar zaman gida, kowa ya fito aiki.” Inji Aregbesola.

A wani jikon kuma, Minister Ayyukan Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Al’umma, Sadiya Farouq, ta ce a rabon kudade da kayan agaji da za a yi ba da dadewa ba, za a maida hankali wajen bayarwa ga masu nakasa ko nakasassun cikin al’umma.

Sannan kuma ta ce za a yi amfani da Gidan Talbijin na Kasa (NTA) da Gidan Radiyo na FRCN a rika koya wa yara ‘yan makaranta darussa, maimakon zaman hirshan a gida.

Idan ba a manta ba, a ranar Litinin ce Ofishin Ministan Ilmi, Adamu Adamu ya fitar da sanarwar cewa dukkan dalibai, tun daga na firamare har zuwa Jami’o’i duk su ci gaba da zaman gida, domin har yau ba a sa ranar sake bude makarantu ba.

Share.

game da Author