Abba Kyari yafi ministoci da hadiman Buhari kaifin kwakwalwa da zurfin tunani – Mamman Daura

0

Daya daga cikin makusantar marigayi Abba Kyari kuma dan uwan shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Mamman Daura ya bayyana cewa marigayi Abba Kyari ya fi duka ministoci da hadiman shugaba Buhari kaifin kwakwalwa da zurfin tunani.

Sannan kuma Abba Kyari mutum ne mai son taimako, da kaskantar da kai ga duk abinda bai sani ba kuma ga shi da natsuwa.

Idan ba a manta Uwargidan shugaban kasa ta rika cewa Mamman Daura da Abba Kyari suna suka kanannade mijin ta sai yadda suke so ake yi.

Sai dai kuma duk da Shugaba Buhari bai nada Mamman Daura wani mukami ba ya na zaune ne a fadar Shugaban Kasa tare da Iyalan sa.

Mamman Daura ya yi juyayin rashin Abba Kyari kuma ya jinjina masa bisa irin ayyukan da yayi wa kasa.

Bayan haka ya bayyana yadda ya fara haduwa da marigayin a Kaduna shekar 47 da suka wuce.

Allah yayi wa marigayi Abba Kyari rasuwa a makon da ya gabata a dalilin fama da yayi da cutar Korona Baros.

An bizne shi a Abuja.

Cutar Korona Baros ta yadu zuwa jihohi 24 a kasar nan. Mutane sama da 900 suka kamu da cutar sannan akalla mutum 197 sun wake sannan 28 sun mutu.

Jihar Legas ce ta fi yawan wadanda suka kamu da cutar, sai babban birnin tarayya, Abuja sai Jihar Kano.

Share.

game da Author