ZAZZABIN LASSA: Mutane 161 sun mutu a Najeriya

0

Hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta sanar cewa daga watan Janairu zuwa 15 ga watan Maris mutane 161 ne suka mutu a kasar nan dalilin kamuwa da zazzabin lassa.

A bayanan da hukumar NCDC ta fidda akalla ma’aikatan kiwon lafiya 34 ne suka mutu a kasar tun da wannan cuta ta bullo a shekaran 2020.

A yanzu dai ma’aikatan kiwon lafiya uku ne suka mutu a jihar Bauchi, daya a jihar Gombe a dalilin kamuwa da cutar.

GINA ASIBITOCI UKU A JIHAR BAUCHI

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammad ya bayyana cewa gwamnati za ta gina cibiyoyin kula da wadanda suka kamu da zazzabin lassa a wasu manyan asibitoci uku dake jihar.

“ Gwamnati ta tsara hanyoyi da zai taimaka waje dakile cutar a jihar sannan muna tabbatar muku da goyan bayan mu 100 bisa 100 a aiyukkan da za kuyi a jihar.

Mohammed wanda matakimakinsa Baba Tela ya wakilce shi a wannan zama yace gwamnati ta kuma bude asusu domin tara kudaden da za a bukata wajen dakile yaduwar cutar a jihar.

Bayan haka shugaban hukumar NCDC Chikwe Ihekweazu ya yi kira ga gwamnati da ta wayar da kan mutane game da hanyoyin samun kariya daga cutar.

Share.

game da Author