Zazzabin Lassa cuta ce da ake kamuwa da ita a dalilin cudanyar bera da abincin da muke ci. Wannan cuta dai a sannu a hankali tana ta afkawa mutanen kasar nan.
Ya kan yi wahala a gano cutar a jikin mutum domin ya kan dauki tsawon kwanaki shida zuwa 21 kafin ta bayyana a jikin mutum.
Za a iya kamuwa da wannan cuta idan aka yawaita zama tare da wanda ya kamu da cutar kuma ba a gaggauta neman magani ba.
An fara gano wannan cuta a Najeriya a shekaran 1969 a jikin wasu ma’aikatan jinya dake aikin jinkai guda uku a kauyen Lassa a jihar Barno.
Wadannan ma’aikatan jinya dai sun rasu a kauyen sannan cutar ya ci gaba da yaduwa.
A yanzu haka duk shekara sai cutar ta sake bayyana inda mutane da dama ke kamuwa kuma da dama ke rasa rayukansu a dalilin cutar.
Rahotanni sun nuna cewa ma’aikatan kiwon lafiya na cikin hadari wajen kamuwa da cutar musamman yadda su ne ke kula da wadanda suka kamu.
Hukumomin kiwon lafiya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga ma’aikatan kiwon lafiya da su rika kula wajen kare kansu a lokacin da suke kula da mutanen da suka kamu da cutar.
Sannan idan aka kwantanta yadda cutar ke yaduwa za a ga cewa mutane sun fi kamuwa da cutar a wannan shekaran fiye da kowacce shekara a baya.
ALAMUN KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA
Ciwon kai: Yawaita fama da ciwon kai alama ne cewa lallai sai an duba mutum a asibiti, domin idan zazzabin lassa ta kama mutum ciwon kai na daga cikin alamun dake fara nunawa.
Zazzabi: Za a rika jin jiki yayi nauyi kamar zazzabi-zazzabi haka idan Lassa ta shiga jikin mutum. Zazzzabi ko masassara zai rika damun mutum a wannan lokaci.
Ciwon jiki: Jikin mutum zai rika yawan yi masa ciwo matuka. Ko ina zai rika jin ciwo yake masa. Hakan ma alama ce dake nuna an kamu da Lassa. Hakna kuma sun hada da ciwon gabobin, ciwon baya, yawan gajiya sannan a wasu lokutan har da ciwon kafafu.
Amai: Saboda zafin zazzabi da ciwon kai mutum kuma zai rika yawan yin amai.
Rashin iya cin abinci: Zazzabin lassa na hana mutum iya cin abinci. zaka ci gaba daya baka bukatan cin wani abu duk ko da cewa zaka rika jin yunwa.
Yawan yin Bahaya: Za a yi fama da yawan shiga bandaki a dalilin kamuwa da wannan cuta sannan hakan zai sa mutum yawan jin kishin ruwa.
Yawaita Suma: Idan har mutum ya kamu da wannan cuta, za a rika yawan suma saboda rashin lafiyar dake jikin mutum.
Jini: Za a rika zubar da jini ta wasu kafafen jiki musamman idan abin ya fara nisa ba a duba mutum a asibiti. Hakan na nuni cewa cutar ta fara yi wa mutum mummunar illa.
YADUWAR CUTAR
WHO ta bayyana cewa a shekaran 2018 mutane 413 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 114 suka mutu.
Hakan ya faru ne a jihohi 21 dake kasar nan wanda suka hada da Abia, Adamawa, Anambra, Bauchi, Benue, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Gombe, Imo, Kaduna, Kogi, Lagos, Nasarawa, Ondo, Osun, Plateau, Rivers, Taraba da Babban birnin tarayya Abuja.
Daga nan kuma a watan Afrilu 2018 ma’aikatan kiwon lafiya 21 ne suka kamu da cutar inda daga ciki takwas suka rasu.
An gano haka ne daga jihohin Abia, Ebonyi, Ondo,Benuwe,Kogi da Nasarawa.
Daga ranar daya ga watan Janairu zuwa 10 ga watan Fabrairu 2019 mutane 324 ne suka kamu da cutar inda daga ciki 70 suka mutu.
Haka ya faru ne a jihohi 20 a kasar nan
A tsakanin wannan lokaci ma’aikatan kiwon lafiya 12 sun kamu da cutar a jihohi bakwai wanda suka hada da Edo, Ondo, Ebonyi,Enugu,Ribas, Bauchi da Benuwe.
Sannan mutun daya daga cikinsu ya rasu a jihar Ebonyi.
A shekaran 2020 hukumar hana yaduwar cututtuka ta kasa (NCDC) ta bayyana cewa an samu karuwan adadin yawan mutanen dake kamuwa da zazzabin lassa da yawan dake mutuwa a dalilin kamuwa da cutar.
Hukumar ta ce daga watan Janairu zuwa Fabrairu mutane 689 ne suka kamu da cutar sannan wasu 118 sun rasu.
An samu wannan yawa ne daga kananan hukumomi 115 dake jihohi 27 a fadin kasar nan.
Har yanzu dai jihohin Edo, Ebonyi da Ondo ne jihohin sa suka fi fama da wannan cuta.
Sannan kuma ma’aikatan kiwon lafiya 20 ne suka kamu da cutar a jihohin Kano,Edo da Ondo.
MATAKAN HANA YADUWAR CUTAR DA GWAMNATI TA DAUKA
Har yanzu dai babu maganin wannan cuta sannan gwamnati ta kasa gano maganin rigakafin cutar da zai taimaka wajen kawar da cutar gaba daya daga kasan.
A shekaran 2020 hukumar NCDC ta kara yawan wuraren yin gwajin cutar da wuraren da masu fama da cutar za su samu kula.
Sannan gwamnatin jihar Ondo wanda ta fi fama da cutar ta mai da yin gwajin cutar da samun kula a jihar kyauta a jihar.
Gwamnatin ta kuma ce za ta ware isassun kudade domin ganin masu fama da cutar a jihar sun samu kula na gari.
KORAFIN DA MUTANE DA MA’AIKATAN KIWON LAFIYA SUKA YI GAME DA YADUWAR ZAZZABIN LASSA
Kungiyar likitoci (NARD) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta ayyana dokar tabaci akan zazzabin lassa ganin yadda cutar ke ta kara yaduwa a kasar nan.
NARD ta yi wannan kira ne gain yadda cutar ke kara yaduwa a bangarorin kasar nan.
Shugaban kungiyar Aliyu Sokomba yace a dalilin haka kungiyar ta ga ya dace gwamnati ta ayyana dokar tabaci a kan cutar domin karfafa matakan hana yaduwar cutar.
Shi ma shugaban Riko na Hukumar EFCC y ace ya na zaton wasu masu binciken kwayoyin cututtuka ne suka kirkiri kwayar cutar zazzabin Lassa da cutar Ebola,
“Wasu mugayen maketatan da keta ta ci zuciyar su da tunanin kwakwalwar su ne suka kirkiro cututtukan
Ya kuma ce rashawa da aikata almundahana ne musabbabin barkewar cutar Coronavirus Chana, har ta bazu cikin kasashen duniya sama da 30.
Hakan da Magu ya fada ya sa aka kallubalancesa da ya yi wa mutane shiru, tun da shi dai ba likita ba ne
Warkewa daga cutar
Har yanzu dai babu wani maganin warkar da cutar balle maganin rigakafin da za a iya yi wa mutane domin su samu kariya daga kamuwa da cutar.
Duk da haka mutanen dake fama da cutar na warkewa daga cutar a asibitoci.
Bayanai sun nuna cewa samun kula ta gari,hutu, cin abincin dake inganta garkuwan jiki,yawn sha ruwa da shan maganin ‘Anti-biotics’ na cikin dabarun da likitoci ke yi dake taimakawa masu fama da cutar warkewa.
Hukumar NCDC ta yi kira ga mutane da su tuntubi likita da zarar mutum ya kamu da zazzabi domin samun tabbacin cutar dake damu mutum.
Hukumar ta kuma ce yin haka na cikin hanyoyin da zai taimaka wa masu fama da cutar warkewa daga cutar.
YADDA ZA A GUJEWA KAMUWA DA ZAZZABIN LASSA
1. Tsaftace Muhalli: A rika tsaftace muhalli a ko da yaushe. A kau da datti a kowani lokaci sannan a rika goggoge wuarare.
2. Zubar da Shara: Idan aka tara datti, kada arika barin su kusa da gida. A kai su can wajen da ake zubdawa a nesa ko kuma a rika konawa.
3. Killace Abinci: Yin haka zai taimaka wajen hana bera ko kwari shiga cikin abincin.
4. Dafa Nama: Kafin a dafa nama kamata a rika wanke shi da ruwan gishiri domin kashe duk wasu kwayoyin cuta dake jikin naman. A tabbatar naman ya dahu sosai kafin a ci.
Namun Daji: A nesanta kai daga yin mu’amula da namun daji musamman jinsin berayaye da birai.
5. Cin ‘ya’yan itatuwa: Kafin a ci ‘ya’yan itatuwa ko kuma ganye a rika wanke su sosai. Hakan na kau da datti a jikin su.
6. A daina barin dabbobin gida na shiga inda ake aje abinci: Kaji da wasu dabbobin da ake kiwon su a gida kan yi mu’amula da beraye a lokutta da yawa.
7. Toshe kafafen da suka bude: A tabbatar an toshe ramin da bera zai iya shiga cikin dakunan mu.
8. Tsafta: A yawaita wanke hannaye da ruwa da sabulu kafin da bayan an ci abinci sannan idan an kammala amfani da ban daki.
9. Ma’aikatan kiwon lafiya su tabbata sun nemi magani da zarar allurar da suka yi amfani da shi a jikin wanda ke dauke da cutar ya soke su.
10. Kona daji: Kona daji na daga cikin hanyoyin dake koro beraye zuwa cikin gidajen mutane. A rika kiyayewa wajen kona dazukan dake kewaye da mu. Mai makon haka a rika feshin magani.
11. Wanke gawa a cikin Daki: Shima hakan na da illa matuka. Maimakon a rika wanke gawa a cikin gida a rika yin sa a waje ne ko kuma inda ya kamata.
Discussion about this post