Wani gungun matasa sun barke da zanga-zanga, inda suka mamaye ofishin Hukumar Hisbah na Kano, su na yin tir da wanda a cikin wani waken sa ya yi izgilanci da batunci ga Annabi Muhammadu.
Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye da rubuce-rubucen da ke nuna suna zargin jami’an tsaro da yin wasarere wajen kin daukar kwakkwaran mataki a kan wanda ya yi izgilancin.
Jagoran masu zanga-zanagar, mai suna Idris Ibrahim, ya shaida cewa sun je ne domin su fada wa gwamnati ta yi abin da ya dace, idan kuma gwamnati ta ki daukar matakin, to su za su dauka da kan su.
Idris ya ce irin wannan ya taba faruwa a Kano a baya, inda wani yay i izgilanci da batunci ga Annabi Muhammadu, amma hukuma ba ta dauki matakin komai a kan sa ba.
Kafin nan, dai wani mai suna Yahaya Sheriff Aminu ne ya yi wata waka inda a ciki ya yi batunci da zagi ga Annabi Muhammadu, wadda ta janyo matasa suka tunzira har suka kai wa iyalan mawakin hari.
Ya dai tsallake ya tsere tun cikin makon da ya gabata.
A ranar Juma’ar da ta gabata ne hasalallun matasa suka banka wa gidan iyayen yaro wuta, wanda ke cikin unguwar Sharifai a cikin birnin Kano, Karamar Hukumar Birni da kewaye.
Mawakin wanda mabiyin darikar Tijjaniyya ne, kuma dan da’irar ‘faidha’, har yanzu bai yi magana a kan abin da ya faru bayan ya yi wakar ba.
Da ya ke yi wa masu zanga-zanga bayani, Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Harun Ibn-Sina, ya ce hukumar sa na bakin kokarin ta, kuma jami’an tsaro sun kama iyayen yaron. Su na can a tsare a hannun ’yan sanda.
Shi ma wanda ya yi magana a madadin Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano, Habu Sani, ya ce su na kokarin damko mawakin wanda ya tsere bayan ya tada kura a Kano.
Wakilin na Kwamishinan ‘Yan Sanda wanda y ace sunan sa Hamza, ya roki a zauna lafiya, a guji tayar da tarzoma.
Ya ce za a yi dukkan abin da ya kamata wajen ganin an kamo wanda ya yi izgilancin an hukunta shi.
[youtube https://www.youtube.com/watch?v=Fm-GC6x_eg8&w=560&h=315]