Kotun Koli ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya shigar ya na neman ta sake duba hukuncin da ta yanke game da Zaben gwamnan jihar Zamfara.
Kotu ta ce Yari ya bata mata lokaci ne kawai nema da yayi ta sake duba hukuncin da ta yanke tun a farko na mika wa PDP kujerar gwamnan jihar.
Kotu ta ce bayan bata mata lokaci da yayi ya bata wa bangaren jam’iyyar da ta shigar da karar kalubalantar zaben, wato bangaren sanata Kabiru Marafa.
Kotu ta ce a dalilin haka sai ya biya Marafa naira miliyan 2 shima na bata masa lokaci da aka yi.
A hukuncin Kotun wadda Justice John Okoro ya karanta ranar Juma’a, ya ce neman a sauya hukuncin da Yari ya nema rashin kunya da cin fuska ga kotun kolin.
” Babu yadda za ayi wai bayan yanke hukunci kuma a dawo wa kotu da wannan batu wai ta sauya hukuncin ta. Hakan akwai rashin kunya da cin fuska.
Idan ba a manta ba, gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari ya nemi ya murde zaben fidda gwani na jam’iyyar APC a shekarar 2019, da hakan ya sa jam’iyyar bata iya yin zaben fidda gwani ba.
Tun daga kotun daukaka kara, aka samu jam’iyyar da laifin kin yin zaben fidda gwani, Amma Yari yaki hakura, ya dage sai ya ga bayan PDP da aka mika wa kujerar gwamnan jihar.
Dama kuma a kwanakin baya, Jam’iyyar PDP ta gargadi kotun koli kada ta kuskura ta yi abinda ba haka ba, domin ko idan ta yi ba daidai ba zata dawo kotun da kararrakin ta wadanda aka kwace mata.
Discussion about this post