ZABEN IMO: Dalilin da ya sa Kotun Koli ta yi watsi da rokon Ihedioha na neman maida shi kan kujerar gwamna

0

Ranar Talata din nan ne Kotun Koli ta yi watsi da rokon da tsohon gwamnan Jihar Imo da ta tsige, Emeka Ihedioha, wanda ya roki kotun ta maida shi kan kujerar sa.

Ya koma kotun ne saboda ya yi zargin cewa alkalan na Kotun Koli su bakwai sun zalunce shi, ba su yi masa adalci ba, saboda sun kwace mulkin jihar daga hannun sa, sun bai wa Hope Uzodinma wanda ya zo na hudu a zabe.

A wannan hukunci da ta kara yankewa, alkalai shida cikin bakwai sun ki amincewa su sake shari’ar. Sun ce babu hurumin yin haka, domin Kotun Koli ba za ta rushe hukuncin da ta yanke da kan ta ba.

Sai dai alkali na cikon bakwai, mai suna Centus Nweze, ya ce Ihedioha ne ke da gaskiya, kuma Kotun Koli ta taba soke shari’ar da ta taba yi a baya.

Nweze ya ce Ihedioha ne halastaccen dan takara, don haka ya kamata INEC ta ba shi takardar shaidar lashe zabe.

Su kuma sauran alkalai shida ba su amince da shi ba.

PREMIUM TIMES a ranar Litinin ta buga labarin yadda Kotun Koli a ranar Litinin 2 Ga Fabrairu, ta dage sauraren karar da tsohon gwamnan Imo wanda ta tsige, Emeka Ihedioha ya koma ya kai mata.

A zaman ta na ranar Litinin din, ta ce za a koma kotu ranar Laraba, 3 Ga Fabrairu, domin ci gaba da sauraren yadda Ihedioha ke neman a dawo masa da hakkin kujerar sa, wadda ya ce Kotun Koli ta kwace daga hannun sa, ta bai wa Hope Uzodinma na jam’iyyar APC da ya zo na 4 a zaben.

A zaman ne na ranar Talata ta kori karar wadda Ihedioha na PDP ya sake garzayawa Kotun Koli ya shigar.

Ihedioha da PDP sun ce Alkalan Kotun Koli sun yi musu bahaguwa kuma gurguwar shari’ar da ba za su iya jira ‘sai lahira a yi musu sakayya ba.’

Don haka suka koma kotun dauke da tulin kididdigar alkaluman zabe masu nuna cewa Kotun Koli ta tabka kuskure, ko dai da gangan ko kuma a bisa rashin sani. Don haka suka ce sai dai a bai wa mai hakki hakkin sa, wato a sake maida wa Ihedioha kujerar sa ya koma kan mulkin Jihar Imo.

Ya bayyana wa kotu ta yi wa Uzodinma aringizon kuri’u kusan 100,000 a lokacin da ta yanke hukunci, kuma kuri’un wadanda babu su a lisaafin wadanda INEC ta tantance a ranar da za a yi zabe.

PREMIUM TIMES HAUSA ta bada labarin yadda babban Lauya Kanu Igabi ya sake garzayawa Kotun Koli, rungume da tulin korafe-korafen hukuncin Kotun Koli da aka tsige wanda ya ke karewa, tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha.

Kotun Koli ta tsige Ihedioha na PDP ranar 14 Ga Janairu, ta maye gurbin sa da dan takarar APC, wanda ya zo na hudu, Hope Uzodinma.

Wannan hukunci ya bai wa dimbin jama’a mamaki, kama daga masana shari’a zuwa wasu daban-daban.

Babban Lauya Kanu Igabi ya dira Kotun Koli tare da sake shigar da karar neman a sake bin kadin shari’ar, domin a cewar sa, tokun ta tabka babban kuskure wajen yanke hukunci.

Dama kuma ita ma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), ta ce ta na nan a matsayin ta cewa Uzodinma bai ci zabe ba. Don haka ba ta gamsu da yadda Kotun Koli ta tsige Ihedioha, ta dora Uzodinma na APC ba.

Dukkan alkalan Kotun Kolin su bakwai dai ne suka amince da tsige Ihedioha da kuma maye gurbin sa da Uzodinma.

Sun ce INEC ta aikata ba daidai ba da ta ki lissafa sakamakon zaben wasu rumfuna 388.

Don haka sai ita Kotun Koli ta yi amfani da sakamakon zaben da ta ce INEC ba ta lissafa da su ba, ta ce Uzodinma ya fi kowa samun kuri’u masu yawa.

Sai dai kuma babban lauya Kanu Igabi ya ce Uzodinma da lauyoyin sa sun yaudari Kotun Koli da sakamakon zabe na bogi, wanda ta yi amfani da shi har ta yanke danyen hukunci.

Yayin da lauyoyin Ihedioha suka hada adadin kuri’un da Kotun Koli ta ce Ihedioha ya samu, to sai ya zama yawan kuri’un da aka kada sun zarce yawan wadanda INEC ta tantance.

INEC ta tantance kuri’u 731,485, amma lissafin da Kotun Koli ta yi ta kara wa Uzodinma kuri’u har ya zama na daya alhali shi ne na hudu, sai ya nuna an jefa kuri’u har 823,743.

A kan haka ne Ihedioha ya koma Kotun Koli, ya ce ba ta yi masa adalci ba. Don haka ya na nema ta mayar masa da kujerar sa.

Dama bayan yanke hukunci an yi ta mamakin yadda Kotun Koli ba ta yi cikakken jawabin ko kuri’u nawa kowane dan takara ya samu daga cikin wadancan rumfuna 388 ba.

Share.

game da Author