Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Abba Kyari ya bayyana cewa yana nan ya na samun lafiya a wajen da ake kula dashi. Sai dai kuma an bashi shawaran a maida shi Legas, cewa a nan ne za afi bashi kula.
Ya ce har yanzu ko zazzabi baya ji a jikin sa duk da ya kamu da cutar coronavirus din.
Idan ba a manta ba, Abba Kyari ya kamu da cutar coronavirus a makon da ya gabata bayan gwajin jini da ya tabbatar da haka.
” Ina so in shaida muku cewa ina nan cikin koshin lafiya amma a killace, kuma a na bani magani da kula kamar yadda ya kamata a dalilin kamuwa da cutar coronavirus da nayi. Za a kuma maida ni garin Legas kamar yadda likitoci suka shawarce ni.
” Ina aiki da matasa masu hazaka, kuma za mu ci gaba da yi wa shugaban kasa aiki tukuru domin ganin gwamnati ta ci gaba da aiki yadda ya kamata.
” Ina matukar godewa ma’aikatan kiwon lafiya, da yan jarida. Sannan kuma ina tabbatar muku cewa shugaba Buhari zai yi iya kokarin sa wajen ganin Najeriya ta ciwo karfin wannan cuta da kuma kare ‘yan kasa.
Yanzu an tabbatar da mutane 111 da suka kamu da cutar a Najeriya.
Discussion about this post