Ministan kiwon lafiya Osagie Ehanire ya bayyana cewa akwai yiwuwar za a iya kamuwa da cutar coronavirus ta hanyar jima’i.
Ehanire ya ce saduwa da wanda ke dauke da cutar na iya sa a kamu da cutar sai dai har yanzu babu binciken da ya tabbatar da haka.
Ministan ya fadi haka ne a taron manema labarai da aka yi a Abuja ranar Alhamis.
Bayan haka wata masaniyar kimiya mai suna Jessica Justman a hiran da ta yi da jaridar ‘The Guardian’ ta kasar Amurka ta ce za a iya kamuwa da coronavirus idan ana yawan kusantan wanda ke dauke da cutar ba sai ta hanyar jima’I ba.
Justman ta ce kungiyar kiwon lafiya ta duniya na Kira ga kasashen duniya da a maida hankali wajen tsaftace muhalli, wanke hannaye da ruwa da sabulu da rage yawan shiga mutane domin guje wa kamuwa da cutar.
Bayan haka Ehanire yace ba kowa bane ya kamata ya saka makarin baki da hanci domin ya ga mutane da dama na amfani da shi domin guje wa kamuwa da cutar.
“Da kowa na bukatan makarin baki da tallafin da gidauniyar Alibaba na Jack Ma ya bada su har miliyan 200”.
Matakai 10 da za a kiyaye domin guje wa kamuwa da CORONAVIRUS
1 – A rika Wanke hannuwa da sabulu a duk lokacin da aka dan wataya ko kuma aka yi tabe-taben abubuwa. Ko bako Kayi ka bashi dama ya wanke hannu kafin ku fara mu’amala.
2 – Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da gefen Hannu amma ba da tafin hannu ba. Idan kun shafi bakunan ku toh, ku wanke hannu maza-maza.
3 – A daina taba idanuwa da hannaye ko kuma hanci da baki. Ka du rika yawan shafa fuskokinku da hannaye. Idana an yi haka a gaggauta wanke hannaye.
4 – A nisanci duk wani da bashi da lafiya, musamman mai yin Mura da tari. Ko zazzabi ne yake yi a nisanta da shi sannan a bashi magani da wuri. Idan abin ya faskara a gaggauta kaishi asibiti domin a duba shi.
5 – A kula da yara sannan a rika tsaftace muhalli.
6 – A rika gaisawa da juna nesa-nesa
7 – Idan kayi bako daga kasar waje, kada a kusance shi koda dan uwana ne sai ya killace kan sa na tsawon makonni biyu.
8 – A rika Karantar da yara yadda za su kiyaye koda an aike su a waje.
9 – A yawaita cin abinci masu gina jiki, shan ruwa da motsa jiki.
10 – A yawaita yin addu’a da sadaka.