Yi wa Sarki Sanusi masauki a garin Awe rahamace gare mu – Mazauna Awe

0

Mazauna garin Awe sun bayyana jin dadin su da aka kawo tsohon sarkin Kano Sanusi garin Awe domin ya zauna. Mazauna garin sun ce wannan abu yayi musu dadi matuka.

Dauda Muhammad-Awa ya ce ” ban ji dadi ba da aka tsige shi daga sarautan Kano sai dai nayi kuma matukar farincikin zaman sa a wannan gari na Awe.

” Mu a wannan gari muna cikin farin iki domin zaman sarki Sanusi a wannan gari rahama ce a gare mu. Saboda kunga yanzu ai garin Awe ya karade ko ina a shafukan jaridu da duniya.

Dauda Ibrahim cewa yayi zuwan Sanusi garin Awe ya sa sun samu karin tsaro a garin. Sai dai yana kira ga gwamnati da ta gyara musu hanyoyoyi.

Ita kuwa Fatima Kande, cewa tayi mutanen Awe za su tabbata sun dadada wa tsohon sarki Sanusi rai da ba zai taba mantawa da zaman sa a wannan gari ba. Wanda ko da ya gama zaman zai rika dawowa yana ganin su akai-akai.

Idan ba manta ba gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya tsige Sarki Sanusi a dalilin wai baya yi wa gwamnati biyayya da karya dokar jihar.

Tuni dai gwamnati ta nata sarkin Bichi, Aminu Ado Bayero sarkin Kano bayan tsige Sanusi.

Share.

game da Author