‘Yan bindigar Kaduna na huce haushin sojoji ne a kan jama’a -Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna rashin Jin dadi da bakin cikin yadda ‘yan bindiga suka kashe mutane 51 a Karamar Hukumar Igabi, cikin Jihar Kaduna.

Mahara sun yi wannan mummunan kisa a ranar Lahadi, inda suka kai mummuman farmaki a kan mazauna yankin Kerawa da wasu kauyuka hudu.

PREMIUM Times Hausa ta bada labarin yadda ‘yan bindigar suka karkashe manya da kananan yara, jira-jirai da almajirai.

Buhari ya ce, “Gwamnati ba za ta mika wuya ga mahara ba, domin su abinda suke so sojoji su daina kai musu hari.

“Ba za a daina fatattakar su ba. Domin rahoton da na samu an ce min, ‘yan bindiga na jin haushin yadda sojoji da ‘yan sanda ke yawan kai musu farmaki sosai.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar, shugaban ya gargadi ‘yan bindiga cewa su bar ganin su na kashe mutane, to akwai ranar-kin-dillanci.

Ya ce gwamnatin sa bakin kokari don tabbatar da nasarar murkushe ‘yan bindiga kakaf.

Ya ce gwamnatin sa ba nan kan bakan ta wajen ganin laifin a ci.gaba da kare rayukan al’immar kasar nan.

Share.

game da Author