Yadda za a iya rabuwa da coronavirus cikin kankanin lokaci – Likitan Chana

0

Wani babban likita kuma mashawarcin gwamnatin kasar Chana kan harkokin kiwon lafiya Zhong Nanshan ya ce duniya za ta iya rabuwa da cutar coronavirus zuwa watan Yuni idan kasashen duniya suka jajirce wajen kiyaye matakan hana yaduwar cutar.

Nanshan ya ce idan har kasashen duniya suka mai da hankali wajen karfafa matakan hana yaduwar cutar kasashen duniya za su rabu da cutar kwata-kwata.

“ Nasarar da aka samu wajen rage yaduwan cutar a Wuhan na da nasaba da mai da hankali wajen karfafa matakan kawar da cutar da gwamnati ta yi ne.

Nanshan ya yi kira ga kasashen duniya da su mai da hankali wajen kiyaye sharuddan kawar da cutar da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bada cewa yin haka zai taimaka wajen kawar da cutar.

Mutane 80,849 ne ke dauke da coronavirus a kasar Chana amma gwamnatin kasar ta ce ta samu ragowar yaduwar cutar a kasar.

A yanzu haka mutane 157,208 sun kamu da cutar wasu 5,842 sun mutu a kasashen duniya 153.

Kasashen Italiya da Iran na daga cikin kasashen da wannan cutar ta yi wa kamun farad daya a duniya.

Share.

game da Author